Sufeto-janar na ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Baba, a ranar Litinin ya shaida sun kama mutune 203 bisa zarginsu da hannu wajen aikata laifukan da suka saba wa dokokin zabe daban-daban.
An kama makamai guda 18 daga hannun ‘yan daban siyasa a yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar kwanaki.
- Zaben Gwamna: NNPP Ta Gargadi Mambobinta Ka Da Su Yi Auren Siyasa Da Sauran Jam’iyyu
- Kotu Ta Bai Wa Atiku Da Obi Damar Duba Takardun Da Aka Yi Zabe Da Su
IGP ya ce, kusan sama da 185 da da ‘yansanda suka kama a sassa daban-daban na kasar nan lokacin gudanar da zaben.
Ya shaida hakan ne a lokacin tattaunawa da jami’an ‘yansanda masu rike da bangarori daban-daban da aka gudanar a shalkwatar ‘yansanda da ke Abuja.
Ya kuma shaida cewa mutanen da ake tuhuma da laifuka daban-daban suna kan matakin bincike a sashin kula da laifukan zabe na ‘yansanda kuma da zarar suka kammala za su mika ga sashin shari’a na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) domin gurfanar da su a gaban kuliya.
A cewar Kakakin ‘yansanda na kasa, CSP Olumuyiwa Adejobi, ganawar an yi ta ne domin tattara bayanan daga jami’an ‘Yansanda don auna kokarin su a lokacin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.
Kazalika, Hukumar ta yi haka don duba wuraren da za a kara azama a kansu domin ganin an tabbatar da tsaro a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da ke tafe a ranar 11 ga watan Maris.