Johnson Fatoki, babba daga cikin wadanda suka tattara sakamakon zaben dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar a jihar Ogun ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Ya sauya shekar ce, kafin zuwan ranar 18 ga watan maris na zaben gwamna da Na ‘yan majalisun dokoki na jihar.
Sauya shekar ta sa, ya janyo wasu da yawa daga jam’iyyun adawa a jihar zuwa bangaren gwamnan jihar, Dapo Abiodun.
Baya ga Fatoki, akwai wasu jiga-jigan PDP a jihar da suma suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Daga cikin su akwai Segun Seriki, Otunba Femi Osifade, Alhaji Saula Adegunwa, Ralph Olaosebikan, Tola Mebude, tsohon sakataren PDP a jihar Bola Odumosun.
Sauran sune, Alhaji T.A. Olatokunbo, Alhaja Fatimo Sonibare, Michael Agbolaade da kuma Akeem Salami.
A na sa jawabin gwamnan jihar Abiodun, ya danganta Fatoki a matsayin jagora kuma mai hangen nesa.
Gwamnan ya kuma yabawa tawagar da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC kan matakin da suka yanke na sauya shekar.