Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, an fafata da shi a zaben fidda gwani na sanatocin yankin Arewacin jihar Yobe.
Abdullahi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci ‘yan jam’iyyar wajen gabatar da zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Wakilin Kamfanin jaridar the nation ya ruwaito.
Ya ce ba zai iya mayar da martani ga duk wani hasashe da ake ta yadawa a kan batutuwan da suka shafi jam’iyyar ba.
Lawan na daya daga cikin ’yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC su 23 da suka fafata a ranar 8 ga watan Yuni.
Bashir Machina dai ya yi ikirarin cewa shi ne sahihin dan takarar kujerar Sanata a yankin Arewacin Yobe.
Da aka tambaye shi tayaya Lawan ya fafafa a takarar Sanata, Adamu ya ce: “Kada ka kai kanka gaban kotu. Waya fada hakan, ko ka ji wasu suna cewa hakan ne?
“Shin akwai wata doka da ta ce idan ka tsaya takara ka fadi ba zaka sake tsayawa wata takara ba?”
“Ku je ku nemo wanda ke da alhakin shirya zaben Fidda Gwanin. Ni na yi iya hurumi na.
“Sai dai ban sani ba a iya sani na, ko ya shiga fafatawar akan lokaci.”