Shahararren malamin addinin musuluncin nan dake zaune a Kaduna, Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Gumi, a ranar Litinin, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi rijistar kada kuri’ar zaben 2023 domin sauya tarihin Nijeriya.
Malamin ya yi gargadin cewa babu wanda ya isa ya yi korafin gwamnati mara gudanar da ayyuka idan har ya kasa kada kuri’a a zabe mai zuwa.
Gumiii, wanda ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook bayan ya sake yin rajistar katin zabensa da ya bata, ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta tsawaita aikin rajistar masu kada kuri’a a yankunan karkara da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira.
Gumi ya kara da cewa bai dace a tauye wa wani dan Nijeriya hakkinsa ba.