Yau Juma’a 10 ga wata, aka gudanar da taro na uku na zaman taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14, inda aka zabi Xi Jinping a matsayin shugaban kasar Sin, da shugaban kwamitin soja na kasar, batun da ya samu goyon baya daga daukacin mambobin majalisar.
Bayan zaben ne kuma shugaba Xi da sabon zababben shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Zhao Leji da mataimakin shugaban kasar, Han Zheng da sauran zababbun manyan jami’ai, suka yi rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar.
Har ila yau a wajen taron, an kada kuri’ar zartar da kuduri kan shirin yin garambawul ga hukumomin majalisar gudanarwar kasar, tare da amincewa da shirin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp