Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya kuma dan takarar gwaman Jihar Kaduna a jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, ya shelanta cewa bai damu da mubayi’ar da sauran jam’iyyun adawa a jihar suka yi wa abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Alh. Isa Ashiru Kudan ba.
Ya sanar da hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na Arise, inda ya yi ikirarin cewa, jamiyyun da suka yiwa Ashiru mubayi’a ba wasu sannnu bane a jihar.
- Gwamnatin Sin Ta Ba Da Tallafin Hatsi Ga Saliyo
- Kotun Koli Ta Umarci INEC Ta Maye Sunan Shekarau Da Hanga
Jamiyyu tara ne dai suka yiwa Ashiru mubayi’a wadanda suka hada da, YPP, AA, APM, APA, APGA, NRM, AP, ADP da da kuma ZLP.
Jamiyyun sun bayyana bara’ar su takarar shugabanni musulmai biyu, inda suka ce, tafiyar za ta raba kan addinai a jihar.
Uba ya ce, mutanen Kaduna na da wayo kuma kansu ya waye haka suna sane da yadda siyasar jihar ke tafiya, inda ya kara da cewa, masu jefa kuri’a a jihar za su fita domin zaba ta a matsayin gwamnan su domin suna sane da irin ayyukan ci gaba da na kawo a jihar da la a mazabata a matsayin sanata.
Uba ya ce, alummar jihar Kaduna sun san Ashiru ya yi zaman majalisar wakilai har na tsawon shekaru takwas, inda kuma alummar suke sane cewa duk tsawon wannan shekaru takwas din, babu wani kuduri daya da Ashiru ya taba daukar nauyi a gaban majalisar wakilai.
Uba ya ce, da wannan ne ya sa nace ban damu da mubayi’ar da jamiyyun suka yiwa Ashiru ba.
—