• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Janye Wa Kowa Takarata Ba – Sani Sha’aban

by Idris Umar
3 years ago
Takarata

Dan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar ADP, Honorabul Sani Sha’aban, ya bayyana cewa maganganun da wasu ke yi cewa ya janye takararsa bai san wannan zancen ba, domin kuwa shi ma ji ya yi kamar al’mara.

Dan takarar, wanda ya bayyana cewa duka ‘yan takarar da ke neman gwamna a jihar Kaduna ‘yan uwa ne domin duk daga Zazzau suka fito, ya bayyana cewa shi bai kullaci kowa ba kuma ba ya da niyyar kullatar wani a zuciyarsa.

  • Jami’in Najeriya: Inganta Samun Wadata Tare Zai Samar Da Karin Kuzari Ga Ci Gaban Kasar Sin
  • Zaben Gwamnoni: Jihohin Da Za A Fafata Mai Tsanani

Dan takarar, wanda ke magana a cikin wata hira da aka yi da shi ta musamman, ya bayyana maganganun janyewar ta sa har sun bata ran cibiyar jam’iyyar ta kasa, inda ya ce, “Abin har ya batawa cibiyar jam’iyyar rai har sun saki sanarwa a kan cewa ADP mai littafi babu inda ta je ta zauna ta ce dantakarar ta ya sauka.”

Ya ma bayyana cewa suna ziyartar juna, ana zumunci tunda ‘yan siyasa suke, amma dai ba a yi yarjejeniya da shi ba.

Dangane da nasararsa, ya bayyana cewa tafiyarsa ta riga ta yi nisa, babu abinda zai cewa Allah sai godiya, inda ya bayyana cewa jam’iyyar LP ta yi karfi a Kaduna, amma kashi 80 sun koma ADP.

LABARAI MASU NASABA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

Da ya ke magana dangane da salon yakin neman zabensa, sai ya bayyana cewa tafiyar 2007 daban ta ke da ta 2011, ita kuma daban ta ke da shekarar 2015, domin a misalin da ya bayar, takarar Buhari akwai lokacin da ake da Boko Haram, akwai lokacin da in za ka tafi Abuja daga Zazzau za ka dunga ganin shingayen sojoji, sai ya ce a kamfe din sa ba ya kwasar motoci masu yawa ya tafi, mutane ke bi wuri zuwa wuri da hotonsa su roki alfarma, ya kan kuma tara mutane na unguwa a sha shayi tare ya gansu su ganshi, ba a ganin tawagarsa domin kada ya sa mutane cikin hadari.

Dan takarar ya bayyana cewa mutane na matukar son takararsa, ana tsayar da shi a gefen titi, a wurin taro, wurin jana’iza a nuna ana so ya fito, wasu ma sun bar jam’iyyun su sun dawo tafiyarsa, inda ya ce kashi 75 na mutanen Kaduna sun yi amanna sun karanta zuciyarsa sun yarda lallai akwai wani nono da zai tarfa a garinsu.

Dan takarar wanda ya yi bayani dangane da irin wahalar da mutane ke fuskanta a bangaren karin kudin makaranta da ilimi, ya bayyana cewa fastocinsa wasu ke yi, huluna da kananan riguna, da tallarsa al’umma ke yi kuma musulmai da kiristoci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NAWIA
Labarai

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Next Post
Jami’in Afirka ta kudu: Tsarin Demokuradiyya Na Sin Ya Mayar Da Hankali Kan Jama’ar Kasar

Jami’in Afirka ta kudu: Tsarin Demokuradiyya Na Sin Ya Mayar Da Hankali Kan Jama’ar Kasar

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.