Tarukan biyu wato NPC da CPPCC da har yanzu ake gudanarwa a nan birnin Beijing na ci gaba da jawo hankulan kasashen duniya. A yayin da yake zantawa da manema labaru na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice a kwanakin baya, Tshilidzi Munya, shugaban kwamitin hada-hadar kudi na lardin Gauteng na kasar Afirka ta Kudu, ya bayyana cewa, tsarin demokuradiyya irin na kasar Sin ya kasance ba kamar dimokuradiyya irin ta sauran sassan duniya ba, dimokuradiyya irin ta kasar Sin ta kan dora muhimmanci kan al’umma.
Kuma jama’ar kasar na shiga cikin harkokin ci gaban kasa, kana suna nan a wani muhimmin matsayi. Ya ce jam’iyyar kwaminis ta Sin da ci gaban kasar a ko da yaushe, suna kasancewa masu mayar da hankali kan jama’a, suna ta kokarin kyautata zaman rayuwar jama’a. Ya kara da cewa, Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan jama’ar kasar, kana tana kokarin hidimtawa jama’arta, abun da ya nuna cewa, tana sanya jama’a a gaban kome. (Mai fassara: Bilkisu Xin)