Farfesa Zakari Ladan na Sashen binciken Pure and Applied Chemistry na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da sauran masu bincike, sun kirkiro wani nau’in maganin cizon sauro.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na KASU, Adamu Bargo, ya fitar a Kaduna ranar Lahadi, ya ce hakan na daga cikin kokarin da ake na kawo karshen annobar zazzabin cizon sauro a Nijeriya.
Bargo ya ce samun nasarar binciken ya samo asali ne daga Tallafin Bincike na sama da Naira Miliyan 27, a karkashin Asusun tallafin Bincike na kasa na 2020 (NRF) na Asusun Tallafawa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund).
“Wannan yana cikin tallafin NRF/TETFund na farko da KASU ta samu a matsayin cibiya mai karbar bakunci, tare da hadin guiwar Jami’ar Bingham da Jami’ar Fasaha ta Vaal, ta Afirka ta Kudu,” in ji shi.
Bargo ya ce, sauran masu binciken sune; Dokta Bamidele Okoli, masanin kimiyyar sinadarai daga Jami’ar Bingham, Dr Uju Ejike, masanin kimiyyar halittu daga jami’ar Bingham da kuma Dokta Mthunzi Fanyana, masani a fannin fasahar nanotechnology daga Jami’ar Fasaha ta Vaal, Afirka ta Kudu.