Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, wadda ke zaman majalisar dokoki ta kasar, ta amince da sabbin ‘yan majalisar gudanarwar kasar ko kuma majalisar ministoci, yayin zamanta na shekara dake gudana yanzu haka.
Bayan gabatar da sunayensu da Firaminista Li Qiang ya yi, mataimakan firaminista da ministoci da gwamnan babban banki da babban mai binciken harkokin kudi da sakatare janar na majalisar gudanarwa ta kasar, sun samu amincewa daga mambobin majalisar NPC na 14, a yayin zamansu na 5, na taronsu na shekara dake gudana.
- Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Watsi Da Ikirarin Fifita Wasu Al’adu Da Cin Karo Na Wayewar Kai
Tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rattaba hannu kan umarnin nada wadannan jami’ai.
‘Yan majalisar NPC sun kuma amince da zaben shugabanni da mataimaka da mambobi 8 na kwamitin musammam na majalisar NPC karo na 14.
Mataimakan firaministan da mambobi da sakatare janar na majalisar gudanarwar kasar, sun sha rantsuwar biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp