An dora kungiyar tsagerun kabilar Igbo da ke fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) akan sikeli na 10 na ‘yan kungiyar ta’addanci a duniya.
A shekarar 2017 ne dai gwamnatin tarayya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci.
Bugu da kari, a shekarar 2023 ne, kungiyar da ke sa ido kan aikata ta’addanci a duniya ta dora kungiyar IPOB a matakin kungiya ta 10 a duniya wajen aikata ta’addanci biyo bayan kai hare-hare 40 da kuma kashe rayukan ‘yan Adam 57 a shekarar 2022.
A cikin rahoton da cibiyar kula da tattalin arziki da kuma kungiyar wanzar da zaman lafiya ta IEP ta wallafa, kungiyar ta’addanci ta IS ce ke kan gaba wajen aikata ta’addanci, inda ta janyo kashe rayukan mutane 1,045 da kai hare-hare guda 410.
Hakazalika, kungiyar ta’addanci ta Al- Shabaab ta kashe rayukan mutane 784 tare da kai hare-hare 315, inda kuma kungiyar ta’addanci ta ISK ta kashe rayukan mutane 498 da kai hare-hare 141.
Har ila yau, kungiyar ta’addanci ta Jama’at Nusrat Al-Islam wal Muslimin ta kashe rayukan mutane 279, inda ta kai hare-hare 77, sai kuma kungiyar ta’addanci ta BLA da ta kashe rayukan mutane 233 da kai hare-hare 30
Kungiyar ISWAP ta kai mataki na shida, inda ta kashe rayukan mutane 219 da kai hare-hare 65 sai kuma kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ta kashe rayukan mutane 219 da kai hare-hare 65 da kuma kashe mutane 204 da kai hare-hare 64.
Rahoton ya kuma nuna cewa, kungiyar ta’addanci ta
Tehrik-e-Taliban da ke kasar Pakistan ta kashe rayukan mutane 137 da kai hare-hare 90 sai kuma kungiyar ta’addanci ta Sinai da ta kashe rayukan mutane 71 da kai hare-hare 27.