Ministan Sadarwa da Inganta Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana yadda hadin gwiwar hukumoni da ke karkashin ma’aikatarsa da suka hada da Hukumar Kula da Sadarwa ta Kasa (NCC), hukumar kula da fasahar sadarwar zamani (NITDA) da Galady Backbone (GBB) za su tabbatar da kare yunkurin yin kutse a intanet ga ‘yan Nijeriya gabanin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zaben 2023.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman ta fitar, Ministan ya bayyana cewa an dakile yunkurin kutse a intanet har sau miliyan 12, wanda hakan ya kara kwarin gwiwa ga ‘yan kasar tare da kai ga gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya cikin gaskiya da adalci.
- Xi Ya Ba Da Sabon Tunani Da Shawarar Wayewar Kai Ta Duniya Don Inganta Zamanantar Da Daukacin Bil-Adama
- Binciken Kayan Zabe: Atiku Ya Janye Sabbin Ƙorafe-Ƙorafe Da Ya Shigar A Kan INEC
Pantami ya kara da cewa matakin ya yi daidai da manufofi da hukumar tsara manufofin tattalin arziki na zamani ta kasa (NDEPS), inda ya kara da cewa bukatar tabbatar da tsaron intanet a Nijeriya ya sanya aka kafa wani tawaga daga hukumar NITDA da za ta dunga amsar bayanan gaggawa daga kwamfuta (CERRT) da kwamitin ba da kulawar kutse na kwamfuta (CSIRT) da cibiyar tsaro ta GBB (SOC).
An kafa cibiyoyin ne tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022, bisa tsarin manufofin ministar kuma sun rika sanya ido a shafukan intanet na Nijeriya kan yiwuwar yin barazana kutse da daukar matakan da suka dace domin dakile su, a dai-daikunsu da kuma a kungiyance tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki.
Sanarwar ta ce, “Yana da kyau a lura cewa, a tunkarar babban zabe na 2023, bayanan sirri sun nuna karuwar barazanar intanet a Nijeriya. Saboda haka, barazanar ga gidajen intanet na jama’a da tashoshinsu sun kai kusan 1,550,000 kowace rana. Duk da haka, wannan ya haura zuwa 6,997,277 a ranar zaben shugaban kasa.
“Ministan sadarwa da inganta tattalin arziki na zamani, a matsayinsa na Farfesa kan tsaro ta intanet kuma wanda ke da sha’awar tabbatar da tsaro da ta yanar gizo, ya umurci duk masu fafutuka da su inganta ayyukan su na awoyi 24 har zuwa kwanaki 7 na hanyoyin sadarwa domin dakile yunkurin kai kutse tun daga ranar 24 ga Fabrairun 2023 zuwa 27 ga Fabrairu 2023.”
Sanarwar ta tuna cewa a ranar 24 ga Fabrairun 2023, ministan ya kaddamar da kwamitin bayar da shawarwari ga taron intanet a Nijeriya da hanyoyin sadarwa na fasahar sadarwa.
Ta ce kwamitin da ke karkashin shugabancin shugaban hukumar NCC, tare da shugabannin NCC, NITDA da GBB a matsayin mambobi, an dora musu alhakkin ayyuka kamar haka, sa ido kan hanyoyin sadarwar don samun nasarar gudanar da sahihin zabe, habakawa da aiwatar da tsare-tsare masu muhimmanci kan ayyukan fasahar zamani, dakile barazanar kutse a intanet, kirkirar hanyoyin da amfani da fasaha, mayar da martani ga hare-haren intanet da kuma dawowa daga duk wani lalacewa da aka yi da sauri.
Sauran sun hada da samar da cikakkiyar tantance hadarin, da yin nazari kan iyawar al’umma ta intanet a halin yanzu, da gano gibin da ya kamata a magance, da kuma ba da shawarwari na kwararru ga gwamnati kan ingantaccen amfani da fasahar zamani wajen gudanar da babban zaben 2023.
“An samu adadin yunkurin yin kutse har 12,988,978, wadanda suka samo asali daga ciki da wajen Nijeriya. Yana da kyau a lura cewa cibiyoyin sun yi nasarar toshe wadannan hare-hare da kuma kara fadada cibiyoyin da hanyar da suka dace.
“Hukumomin karkashin kulawar ma’aikatar sadarwa da inganta tattalin arziki na zamani sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da yanayi mai dacewa don samun nasarar gudanar da sahihin zabe.
“Ministan ya yaba wa duk masu ruwa da tsaki a tsarin inganta tattalin arzikin zamani don goyon bayansu wanda ya haifar da wannan nasarar da ba a taba samu ba. Abu mafi muhimmanci shi ne, ministan ya lura cewa wadannan nasarorin sun samo asali ne sakamakon jajircewar gwamnatin Shugaba kasa Muhammadu Buhari, na tabbatar da samun nasarar sauye-sauyen da Nijeriya ta samu a fannin tattalin arziki na zamani.
“Sashin inganta tattalin arzikin zamani ya sami ci gaba da goyon bayan shugaban kasa kuma abun a yaba ne. Ya kuma yi fatan za a yi amfani da darussan da aka koya a lokacin aikin yadda ya kamata a zabukan da ke tafe”.