Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Bauchi a jam’iyyar NNPP, Sanata Halliru Dauda Jika, ya ce, alamu na nuni da cewa shi ne zai lashe zaben gwamnan Jihar.
Jika da ke wannan maganar bayan kada kuri’arsa a mazabarsa da ke Buri 2 Women Center Kafin Madaki da ke karamar hukumar Ganjuwa, ya jinjina wa hukumar zabe INEC bisa yadda aka samu sauyi wajen tafiyar da aiki cikin hanzari.
- Zaben Gwamnoni: Ku Ankare Akwai Masu Shaidar Aikin Tsaro Ta Bogi, INEC Ga Masu Zabe
- Dandazon Jama’a Sun Fito Jefa Kuri’a A Zaben Gwamna A Bauchi
Ya ce, da tantance mutum har zuwa ya kada kuri’arsa mintina kadan sun isheshi, don haka ne ya yi fatan za a kammala zaben cikin koshi lafiya.
Kazalika, ya nuna gamsuwarsa kan yadda jama’a suka fito sosai domin kada kuri’a a yayin zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar a yau Asabar.