Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Ekiti, Otunba Bisi Egbeyemi, ya rasu.
An ruwaito cewa ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Asabar bayan ya sha fama da gajeruwar rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 79.
- Ina Da Kwarin Guiwar Lashe Zaben Gwamnan Bauchi -Sanata Jika
- Zaben Gwamnoni: Ku Ankare Akwai Masu Shaidar Aikin Tsaro Ta Bogi, INEC Ga Masu Zabe
Egbeyemi, wanda aka haifa a ranar 8 ga watan Mayu, 1944, ya zama mataimakin gwamna ga tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, daga 2018 zuwa 2022.
Ko da yake, babu wata sanarwa a hukumance daga iyalansa, gwamnatin jihar da kuma jam’iyyarsa ta APC, amma wata majiya mai tushe daga jihar ta tabbatar da mutuwarsa.