Kwamishinan zabe na Jihar Kuros Riba, Farfesa Gabriel Yomeri, ya tabbatar da cewa ma’aikaciyar wucin gadi ta INEC, Miss Glory Effiom Essien, wacce harsashi da ake zargin ‘yan bindiga ne ya same ta, yanzu haka na samun sauki a asibitin koyarwa na Jami’ar Kalaba.
Rahotanni sun ce an harbe ta ne a bayanta a cikin wani jirgin ruwa mai sauri da ke tafiya zuwa yankunan Bakassi domin gudanar da zabe.
- Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Yobe Ya Rasa Kujerarsa A Wajen Nguru
- Ina Da Kwarin Guiwar Samun Nasarar Tazarce -Matawalle
Hukumar ta nuna damuwa da bacin rai game da harbin da aka yi wa budurwar.
Sai dai, ya ce ya yi farin ciki cewa harsashin bai shafi kashin bayan wadda abin ya shafa ba.
“Wadda abun ya shafa na samun kulawar likita a Jami’ar Kalaba (UCTH).”
Wani ganau ya ce, “harsashin ya same ta ne a lokacin da take cikin wani jirgin ruwa mai sauri da ya nufi yankin Bakassi domin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki.
Ta fadi kafin a garzaya da ita asibiti.
“Ta fadi sannan ta suma kafin kai ta asibiti don yi mata magani.”