Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar PDP na gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ayyana dan takarar jam’iyyar APC Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.Â
Jagororin zanga-zangar, Hon. Maria Dogo da Hajiya A’isha Ibrahim Madina, sun ce an yi musu fashi da rana tsaka, kuma suna kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta sake duba sakamakon zaben tare da ayyana Hon. Isa Ashiru Kudan na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Matan sun bayyana sakamakon zaben a matsayin fashin rana tsaka, inda suka jaddada cewa mutanen jihar Kaduna sun bayyan a fili suna goyon bayan jam’iyyar PDP.
Matan sun gudanar da zanga-zangar ne a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya NUJ a Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp