Majalisar Dokokin Jihar Kogi, ta dakatar da ‘yan majalisa tara bisa zargin ayyukan ta’addanci da laifukan zabe.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne a ranar Alhamis a wani karamin zama da shugaban majalisar, Prince Mathew Kolawole ya jagoranta, inda shugaban ya karanta wasikar da gwamnan Jihar, Yahaya Bello ya tura wa majalisar kan zargin ‘yan majalisar da aikata ta’addanci.
- Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane
Har ila yau, majalisar ta dakatar da shugabanin kananan hukomomi bakwai bisa zarginsu da tayar da rikici a lokacin zabe.
‘Yan majalisar da abin ya shafa su ne, Olusola Kilani, Bello Hassan, Muhammed Lawi Ahmed, Moses Akande
Aderonke Aro, Daniyan Ranyi, Atule Igbunu, Atachaji Musa, Muktah Bajeh.
Shugabanin kananan hukomomin da aka dakatar su ne na Bassa Hon Muktari Shaibu da mataimakin sa, shugaban karamar hukumar Ogori/Magongo Hon. Okparison da mataimakin sa; shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma Hon Pius Kolawole; shugaban karamar hukumar Ibaji Kabba/Bunu Hon. Moses Olorunleke da mataimakinsa Adebimpe Alfred; Mustapha Akaaba shugaban karamar hukumar Ajaokuta, Joseph Salami shugaban karamar hukumar Adavi.
Majalisar ta kuma dakatar da shugaban karamar hukumar Lokoja Hon. Dansabe Muhammed bisa zarginsa da almundahanar kashe kudi ba bisa ka’ida ba da suka kai Naira miliyan150.
A bayanansu dangane da zargin mataimakin shugaban majalisar Hon. Alfa Rabiu Momoh ya goyi bayan dakatar da ‘yan majalisar tara.
Majalisar ta kuma kafa kwamitin wucin gadi a karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar domin bincikar zargin.