Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC, Nasiru Yusif Gawuna ya taya al’ummar Musulmin Kano da sauran al’ummar kasa murnar fara azumin watan Ramadan mai alfarma.
A cewarsa, “Yayin da muka fara azumin watan Ramadan addu’armu ita ce fatan yin koyi da kyawawan koyarwar da ke cikin wannan wata mai alfarmar tare da riko da koyarwar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, musamman adalci, soyayya, hakuri, zaman lafiya da sadaukar da kai.
- NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya
- NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya
“A Musulunci watan Ramadan na bayar da da damammaki ga Musulmi domin kara sadaukar da kai wajen bautawa Allah madaukakin Sarki.
“Ya zama wajibi mu kara himmatuwa wajen amfani da wannan wata wajen kara jajircewa da bautawa Allah.
“Muna addu’ar Allah ya karbi ibadunmu da za a gudanar a wannan wata tare da samun kyakkyawan sakamako.”
Haka zalika Gawuna ya bukaci al’ummar Musulmi da sauran jama’ar kasa da su yi amfani damar da ke kunshe a wannan wata domin kara jajircewa wajen addu’o’i domin dorewar zaman lafiya.
Kamar yadda daraktan yada labaran mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADERSHIP Hausa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp