Daga ranar Litinin zuwa ta Laraba na wannan mako, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai ziyara a kasar Rasha, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, wadda ta kasance ziyara ta farko da shugaban na kasar Sin ya kai a bana.
Dangane da ziyarar shugaba Xi, jama’a daga kasashe daban daban sun bayyana cewa, ziyarar mai matukar muhimmanci, ta nuna yadda kasar Sin ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya, da yadda kasar ke taka muhimmiyar rawa, a matsayinta na babbar kasa, don samar da kwanciyar hankali ga al’amuran kasa da kasa masu sarkakiya. Kana ziyarar za ta taimakawa kokarin bangarori daban daban masu fada a ji a duniya, da kare tsari na dimokuradiya tsakanin kasashe daban daban.
Shugaba Xi ya ziyarci kasar Rasha shekaru 10 da suka wuce, yayin da ya fara aiki a matsayin shugaban kasa. Sa’an nan a wannan karo ya sake mai da Rasha a matsayin zango na farko na kai ziyara, bayan da ya samu wani sabon wa’adin mulki. Wannan wani kuduri ne na siyasa da aka yanke bayan nazari mai zurfi, kuma tafiya ce ta sada zumunci da hadin gwiwa da zaman lafiya mai ma’ana dake cike da tarihi.
Duk da yanayi mai muhimmanci da damuwa da da rudani da ake fuskanta a duniya, amma shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kokarin samar da wani yanayi na tabbaci, ta hanyar aiwatar da manufar diplomasiya ta kasar Sin mai dorewa. (Bello Wang)