Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta dakatar da shugaban karamar hukumar Chikun, Salasi Musu da takwaransa na karamar hukumar Giwa, Abubakar Lawal, bisa zargin badakalar kudade.
‘Yan Majalisun sun dauki wannan matakin ne a zamansunna ranar Talata biyo bayan wani kudirin da Honorable Ahmed Chokali mai wakiltar mazabar Zaria Kewaye.
A cewar dan Majalisar, ba za su cigaba da zura ido suna kallon shugabanni kananan hukumomin suna cigaba da kauce wa dokoki da ka’idojin kananan hukumomin da jihar ke tafiya a kai.
Mr Chokali ya gabatar da kudirin inda kuma Majalisar ta amince da kaddamar da bincike kan lamarin.
“Na tashi a gaban Majalisar domin gabatar da kudiri da zai bada damar gudanar da bincike bisa sashin doka na 128 na kundin tsarin mulkin Nijeriya don a binciki harkokin kananan hukumomin guda biyu.”
Daga bisani Majalisar ta shawarci dakatartun shugabannin kananan hukumomin da su bada cikakken dama domin a gudanar da binciken da suka kamata.