Iyalan ‘Yan Nijeriya akalla 39 ne ke zaman makokin mutanen da aka kashe a zaben 2023, a daidai lokacin da wasu ‘yan siyasa ke murnar samun nasarar zaben su.
Wadanda suka mutu a zabukan shugaban kasa da na gwamna da aka gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 18 ga Maris, 2023 sun hada da ‘yan sanda, ‘yan siyasa, ’yan bangar siyasa da ma wadanda har yanzu ba a san ko su wane ne ba har yanzu.
- Zaben Gwamna: PDP Za Ta Yi Zanga-Zangar Kwana 7 Kan Sakamakon Zaben NasarawaÂ
- Kotu Ta Karbi Kararrakin Zabe 6 A Kebbi
A Kano, dan majalisar wakilai mai ci, Ado Doguwa, tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu kan rikicin ranar zabe da ya yi sanadin mutuwar ‘yan mazabarsa uku.
Yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sha alwashin kamawa tare da gurfanar da wadanda suka haddasa tashe-tashen hankula a zaben da dama.
A karshen makon da ya gabata ne LEADERSHIP ta yi nazari kan wasu daga cikin shari’o’in da suka hada da wadanda aka yi ta yadawa a kafafen yada labarai ko kuma ‘yan sanda suka tabbatar a jihohin da suka samu munanan tashe-tashen hankula da suka shafi zabe.