Siyasar Kano ta sha bamban da siyasar sauran jihohin da ke Nijeriya, domin salon siyasar ya zama tamkar hannun karba, hannun mayarwa, wannan kuwa baya rasa nasaba da irin tsayuwar dakan jama’ar Kano kan akidarsu.
Tun jamhuriya ta biyu idan za a tuna an ga yadda Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi karansa yakai tsaiko, ta yadda idan ka cire Malam Aminu Kano, ba wani dan siyasa a Kano da ake jin duriyarsa a kakar zaben shekara ta 1979. Haka Muhammadu Abubakar ya samu nasarar lashe zaben Gwamnan Jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PRP, wanda ya shugabanci Kano tsawon shekara hudu.
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
- Shema Ya Bai Wa PDP Sa’o’i 48 Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Masa
A kokarin neman tazarce ne, Alhaji Muhammadu Anbubakar Rimi ya samu matsalar da malaminsa a siyasance, Malam Aminu Kano wanda hakan ya sa ya fita ya kafa sabuwar jam’iyyar NPP (canji), yayin da shi kuma Marigayi Sabo Bakin Zuwo ya samu tikitin takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PRP, wannan fafatawar ce ta bai wa Sabo Bakin Zuwo nasarar darewar kujerar gwamnan Kano a shekara ta 1983, kafin daga bisani sojojin su yi juyin mulki.
Tun daga wannan lokaci ne siyasar Kano ta sha bamban da siyasar sauran jihohi, musamman ta fuskar kekasa kasar da Kanawa suka shahara a kai idan suka juyawa kowane irin lamari baya.
Shi ma Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya ya samu damar lashe zaben gwamna zango farko karkashin tutar jam’iyyar NRC, wanda shi ma ba su cika shekara biyu ba aka hambarar da gwamnatin tasu.
Bayan dawowar dimokuradiyya a shekara ta 1999 lokacin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu damar zama gwamna a jam’iyyar PDP, inda ya jagoranci Jihar Kano tsawon shekara hudu tun daga 1999 zuwa 2003, shi ma yana kan sharafinsa wanda bai taba zaton faduwa a zaben shekara ta 2003 ba, amma saboda salon siyasar jama’ar jihar Kano, suka juya masa baya tare da zabar tsohon malamin makaranta, Malam Ibrahim Shekarau a karkashin tutar jam’iyyar ANPP, wanda ya kwace mulki daga hannu jam’iyya mai ci ta PDP.
A karon farko, Malam Ibrahim Shekarau ne ya fara karya kofin Kanawa da ake cewa ba a mulkar Kano karo na biyu, tsohon malamin makarantar ya samu nasara a zagon farko daga shekara ta 2007 zuwa 2015, kwatsam a lokcin zaben shekara ta 2015, Injiniyar Rabi’u Musa Kwankwaso ya sake kwace mulkin daga hannun Shekarau bayan ya kammala zango biyu a kan karagar mulkin Kano, inda aka tsayar da Malam Salihu Sagir Takai wanda ya sha kashi a hannun jam’iyyar PDP, kasancewar zango biyu mutun ke iya yi ya sa bayan kammala shekara hudun Kwankwaso aka tsayar da mataimakinsa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bayan an sha fama, saboda a lokacin Kwankwaso bai so ba shi takarar ba, haka dai aka yi Allah ya bai wa Ganduje dama a zango farko.
 Kokarin neman tazarcen Ganduje ne a karon farko aka gamu da rashin kammalar zabe (Inconclusibe), wannan tataburza tasa da kyar Ganduje ya kai bantensa, wanda wannan nasara ce ta ba shi damar samun tazarce, inda ya cika shekara takwas a kan karagar mulkin Kano.
A zaben da aka kammala mako guda da ya gabata wanda aka fafata matuka, domin yadda jam’iyyar adawa ta NNPP karkashin limamin kwankwasiyya suka shata layi tare da yin amfani da damar tallata hajarsu ta hanyar kawo babbar matsalar sauyin kudade da kuma tsadar kayan masarufi da tsadar man fetur, wanda tasa takarar ta yi mummunan zafi tsakanin jam’iyya mai mulki ta APCÂ da jam’iyyar NNPP, tun a zaben shugaban kasa wanda Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wa jam’iyyar tasa ta NNPPÂ takarar shugabancin kasa ya samu nasara kan sauran ‘yan takarkaru a matakin jiha. Wannan tasa a zaben gwamna suka samu yakinin cewa lallai su ne da nasara idan an zo zaben gwamna. Hakan tasa zaben ya yi zafi matuka, amma daga karkashe jam’iyya NNPP ta samu nasara lashe zabe da rinjye mai yawa.
Jam’iyyar APC a Kano ta bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kwanaki 7 ta gaggauta ayyana zaben gwamna a matsayin wanda bai kammala ba.
Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana sakamakon zaben da aka kammala wanda aka ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya yi nasara da cewa ba shi da tushe balle makama kuma bai inganta ba.
Lauyan jam’iyyar APC, Abdul Fagge ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Talata, ya ce ba yadda za a iya bayyana sakamakon zaben da aka soke kuri’a 270,000 wanda ya nuna tazarar da ake ikirarin cin zaben da su ba su kai adadin kuri’un da aka soke ba.
Ya ce, “Idan aka yi la’akari da sashi na 65 na dokokin zabe na shekara 2022, mun rubuta wa hukumar zabe mai zaman kanta cewa ta sake nazari tare da soke wannan sakamakon na son zuciya, wanda aka bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP tare da bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammala ba”.
Lauyan jam’iyyar APC wanda ke tare da dan takarar Gwamnan Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da jiga-jigan jam’iyyar APC, ya bayyana cewa jami’in da ya tattara sakamakon ya yi gaban kansa ne amma bai yi aiki da dokar zaben ba.
A lokaci guda kuma, Lauya Abdul Fagge ya yi tsokaci da tanadin dokar zabe da ta bayyana cewa idan aka samu tashin hankali. Fagge ya ce idan har hukumar zaben Jihar Kebbi da Adamawa za su ayyana zabukan su a matsayin wanda bai kammala ba, me ne dalilin da zai hana daukar irin mataki a Kano wanda aka tabbatar da hatsaniya a cikinsa?
Shi ma da yake jawabi a lokacin taron manema labaran, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya, Alhassan Ado Doguwa cewa ya yi an soke zabensa ne da irin abin da ya faru a zaben gwamnan Kano, amma aka ayyana nasa zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Doguwa ya kara da cewa daga cikin akwaruna 13, an soke 12 bisa zargin hatsaniya da aringuzon kuri’a, ya kuma karbi wannan hukuncin, sannan yana jira ranar da za a sake zaben.
Sai dai kuma tun bayan sanar da sakamakon gwamnan ne da hukumar zaben Jihar Kano ta bayyana, Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, sai magoya bayan sa suka fantsama kan tituna.
A wani salon murnar lashe zabe, wasu bata-gari suka afka wa kadarorin mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ciki har da gidansa da ke kan titin Masallachin Sabilul Rashad, inda aka kone wasu motocinsa tare da banka wa wani sashe na gidan wuta. Haka kuma matasan sun afka wa ofishin Rararan da ke daura da gidan adana namun daji (Zoo) suka kwashe duk wani abu mai amfani da ke ofishin.
Shi ma Baban Chenedu ya koka kan yadda wadannan matasa suka afka gidansa, inda ya ce sun yi masa asarar abin da ya haura naira miliyan 10 tare da sassara kaninsa wanda ya ce shi ba ma ya ra’ayin siyasa baki daya.
Ita ma a na ta bangaren, rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta shelanta damke wasu da ake zargi da hannu cikin aikata wannan ta’asa. Rundunar ta dakile duk wani yunkurin ta da zaune tsaye a Kano.
Zuwa yanzu dai hankali ya kwanta a Jihar Kano bayan sanar da janye dokar ta-baci da gwamnati ta kakaba.