Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga dandalin tattauna harkokin samar da ci gaba na kasar Sin wato CDF na shekarar 2023 a yau Lahadi.
A cewar shugaba Xi, a yanzu haka, ana samun manyan sauye-sauye, wadanda ba a gansu ba cikin karni a fadin duniya, kana ana samun rikici da rashin kwanciyar hankali a shiyyoyi akai-akai, sannan farfadowar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya. Inda ya ce kyautata farfadowar tattalin arzikin duniya na bukatar hadin gwiwa da cimma matsaya guda.
Xi Jinping ya kara da cewa, shawarar raya ci gaban duniya da Sin ta gabatar, ta samu goyon baya da yabo sosai, daga al’ummun kasa da kasa.
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin za ta ci gaba da jajircewa kan manufar kasar ta bude kofa ga kasashen waje, da neman cimma moriyar juna ta hanyar bude kofa da ci gaba da samar da sabbin damarmaki ga duniya ta hanyar sabbin nasarorin ci gaba da za ta samu.
Taken dandanlin CDF na bana da aka bude yau Lahadi a birnin Beijing shi ne, “Farfadowar Tattalin arziki: Damarmaki da Hadin Gwiwa”. Cibiyar binciken hanyoyin ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin ce ta karbi bakuncin taron. (Fa’iza Mustapha)