A yau Lahadi, kasashen Sin da Honduras, suka sanar da kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu, wanda ke kunshe cikin wata sanarwar hadin gwiwa da bangarorin biyu suka rattabawa hannu, a birnin Beijing.Â
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Qin Gang da takwaransa na Honduras, Eduardo Reina ne suka rattaba hannu kan sanarwar bayan tattaunawar da suka yi.
A cewar sanarwar, bisa la’akari da muradu da bukatun al’ummomin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da Jamhuriyar Honduras, kasashen biyu sun yanke shawarar amincewa da juna da kuma kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu, wanda zai fara aiki daga yau Lahadi, ranar da aka rattaba hannu kan wannan sanarwa.
Haka kuma, gwamnatocin kasashen biyu sun amince su kulla huldar abota a tsakaninsu bisa ka’idojin mutunta cikakken ‘yanci da iko da yankunansu da kaucewa fito-na-fito da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan juna da tabbatar da daidaito a tsakaninsu, da kuma mu’amala cikin zaman lafiya.
Bugu da kari, gwamnatin Honduras ta ce ta amince da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ce halastacciyar gwamnati dake wakiltar baki dayan kasar, kuma Taiwan wani bangare ne na kasar da ba zai iya ballewa ba.
Har ila yau, gwamnatin Honduras ta ce za ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan, kuma ba za ta kara kulla wata hulda ko musaya a hukumance tsakaninta da Taiwan ba. (Fa’iza Mustapha)