Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Honduras, mataki ne na siyasa, kuma bisa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, wadda ba ta tattare da wasu sharudda.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka a yau Litinin, a lokacin da aka yi mata tambayar ko Sin za ta ba Honduras kudin da ya kai kusan dalar Amurka biliyan 2.5 da ake zargin Honduras din ta nema daga yankin Taiwan.
Mao Ning ta amsa da cewa, kulla huldar diflomasiyya ba batu ne na ciniki ba, tana mai cewa, a baya-bayan nan, kasashe kamar Panama da Jamhuriyar Dominican da El Salvador da Nicaragua da sauransu, sun kulla ko sun dawo da huldar diflomasiyya da kasar Sin ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
A cewarta, bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Honduras, bisa ka’idojin kasancewar Sin daya tilo a duniya da mutunta juna da yin zaman daidai wa daida da neman moriyar juna, da kuma neman ci gaba na bai daya, Sin za ta inganta hadin gwiwar moriyar juna da Honduras a mabambantan fannoni, domin taimakawa kasar raya tattalin arziki da zamantakewa tare da samar da moriya ga al’ummarta. (Fa’iza Mustapha)