ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubakar Malami Ya Fice Daga APC, Ya Koma ADC

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Abubakar

Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya kuma ɗan jihar Kebbi, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana mai cewa matakin ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma nazari na ƙashin kai. A wata sanarwa da ya fitar ranar 2 ga Yuli, 2025, Malami ya bayyana komawarsa jam’iyyar ADC – jam’iyyar da ke jagorantar sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa.

Malami ya ce ba fushi ko son mulki ne ya jawo masa wannan mataki ba, illa kawai damuwa da ƙaunar ƙasa da kuma wahalhalun da al’ummar Nijeriya ke ciki. Ya bayyana cewa Nijeriya na cikin mawuyacin hali, inda rashin tsaro ya yi kamari, musamman a Arewacin ƙasa, yayin da gwamnati ke fifita siyasa akan tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

  • Fitaccen Malamin Musulunci Mai Da’awar Sunnah A Nijeriya, Dr. Idris Dutsen Tanshi Ya Rasu
  • Tarihin Makarantar Katsina-kwalej Zuwa Ta Horon Malamai (1)

Ya kuma caccaki halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, yana mai cewa hauhawar farashin kayan masarufi da rashin aikin yi sun kai matakin da talakawa ba sa iya ciyar da iyalansu. Ya zargi gwamnati da watsi da shugabanci, inda ya ce rabon muƙamai da aiwatar da manufofi yanzu yana bisa biyayya ta siyasa, ba ƙaunar ƙasa ba.

ADVERTISEMENT

A ƙarshe, Malami ya ce matakin da ya ɗauka na komawa ADC wata hanya ce ta dawo da adalci, da cancanta, da haɗin kai da farfado da ƙasa.

Ya tabbatar wa mutanen jihar Kebbi da cewa zai ci gaba da kasancewa da su, yana kare muradunsu da muradun Nijeriya gaba ɗaya. Ya yi kira ga ’yan Nijeriya su haɗu don ceto ƙasar daga durƙushewa.

LABARAI MASU NASABA

An Kai Wa Kwankwaso Hari Tare Da Jikkata Wasu A Kano

SERAP Ta Bai Wa INEC Wa’adin Kwanaki 7 Ta Gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Rikicin Siyasa

Abubakar
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Shehu Buba Ya Zargi Gwamnan Bauchi Da Bai Wa Kansa Da Iyalansa Kwangiloli
  • Abubakar Sulaiman
    SERAP Ta Bai Wa INEC Wa’adin Kwanaki 7 Ta Gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Rikicin Siyasa
  • Abubakar Sulaiman
    ICPC Za Ta Fara Wallafa Sunayen Mamallakan Kadarorin Da Ta Ƙwace
  • Abubakar Sulaiman
    Ƙasar Italiya Ta Ci Tarar Facebook Yuro Miliyan 805

MASU ALAKA

2027: NDC Za Ta Duba Yiwuwar Dawo Da Tallafin Man Fetur Domin Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya
Siyasa

An Kai Wa Kwankwaso Hari Tare Da Jikkata Wasu A Kano

November 15, 2026
SERAP Ta Bai Wa INEC Wa’adin Kwanaki 7 Ta Gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Rikicin Siyasa
Labarai

SERAP Ta Bai Wa INEC Wa’adin Kwanaki 7 Ta Gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Rikicin Siyasa

November 15, 2026
ICPC Za Ta Fara Wallafa Sunayen Mamallakan Kadarorin Da Ta Ƙwace
Manyan Labarai

ICPC Za Ta Fara Wallafa Sunayen Mamallakan Kadarorin Da Ta Ƙwace

November 15, 2026
Next Post
Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma

Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma

LABARAI MASU NASABA

2027: NDC Za Ta Duba Yiwuwar Dawo Da Tallafin Man Fetur Domin Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya

An Kai Wa Kwankwaso Hari Tare Da Jikkata Wasu A Kano

November 15, 2026
Shehu Buba Ya Zargi Gwamnan Bauchi Da Bai Wa Kansa Da Iyalansa Kwangiloli

Shehu Buba Ya Zargi Gwamnan Bauchi Da Bai Wa Kansa Da Iyalansa Kwangiloli

November 15, 2026
SERAP Ta Bai Wa INEC Wa’adin Kwanaki 7 Ta Gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Rikicin Siyasa

SERAP Ta Bai Wa INEC Wa’adin Kwanaki 7 Ta Gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Rikicin Siyasa

November 15, 2026
ICPC Za Ta Fara Wallafa Sunayen Mamallakan Kadarorin Da Ta Ƙwace

ICPC Za Ta Fara Wallafa Sunayen Mamallakan Kadarorin Da Ta Ƙwace

November 15, 2026
CMG Da MDD Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna

CMG Da MDD Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna

November 15, 2026
Ƙasar Italiya Ta Ci Tarar Facebook Yuro Miliyan 805

Ƙasar Italiya Ta Ci Tarar Facebook Yuro Miliyan 805

November 15, 2026
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Yin Kokari Wajen Gina Al’ummar Asiya Da Tekun Fasifik”

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Yin Kokari Wajen Gina Al’ummar Asiya Da Tekun Fasifik”

November 15, 2026
Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Balaguron Fasinjoji Sau Biliyan 4.13 A Cikin Watanni 10 Na Farkon 2026

Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Balaguron Fasinjoji Sau Biliyan 4.13 A Cikin Watanni 10 Na Farkon 2026

November 15, 2026
Shugabanni 12 Na Yankunan Tattalin Arzikin Kungiyar APEC Za Su Halarci Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na 2026

Shugabanni 12 Na Yankunan Tattalin Arzikin Kungiyar APEC Za Su Halarci Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na 2026

November 15, 2026
Ƴan Bindiga Sun Harbe Hadimin Gwamnan Zamfara Har Lahira

Ƴan Bindiga Sun Harbe Hadimin Gwamnan Zamfara Har Lahira

November 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.