Kasa da sa’o’i 24 da rasa rayukan mutane 11 a hanyar Mokwa zuwa Lapai a Jihar Neja, wasu mutane 24 sun mutu a wani hatsarin mota da auku a hanyar Kutigi zuwa Bida a jihar.
Wani ganau ya shaida wa LEADERSHIP cewa hatsarin ya auku ne da tsakar daren ranar Talata a kauyen Etsuworo, inda wata babbar mota ta taso daga Zariya zuwa Jihar Legas.
- Kotun Tarayya Ta Kori Dan Majalisar Adamawa Daga Mukaminsa
- Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Dakatar Da Ayu Daga Shugabancin PDP
Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa mutane 24 ne suka mutu a hatsarin, kuma an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kutigi, da ke hedikwatar karamar hukumar Lavun ta jihar.