A martaninta dangane da taron da ake kira da “Taron Demokradiyya” da kasar Amurka ta karbi bakuncinsa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta jaddada yayin taron manema labarai na yau Talata cewa, kasar Sin na kira ga Amurka ta daina fakewa da batun demokradiyya, tana yi wa kasashen duniya katsalandan cikin harkokinsu na cikin gida.
Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar wakilan kasar Amurka za ta sake nazartar dokar sa ido kan wayoyin sadarwa da aka shimfida a karkashin teku, wanda kwamitinta ya zartar a baya. Dokar na da nufin hana masu takara na kasashen waje, samun fasahohi da kayayyakin dake da alaka da wayoyin sadarwa na karkashin teku. A martaninta, Mao Ning ta ce kasar Sin na adawa da yadda Amurka ke yin kudin goro ga batun tsaron kasa da kuma yadda take danne kamfanonin kasashen waje bisa dalilai mara ma’ana.
Har ila yau, wasu rahotanni sun bayyana cewa wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana manhajar TikTok a matsayin wani babban kalubale, yana mai kwatanta ta da manhajar kutse. A martaninta, Mao Ning ta ce abun da Amurka ta yi ba lalata muradun kamfanoni da jama’ar kasar kadai ya yi ba, har ma da zubar da kimar kasar da sanyaya gwiwar masu zuba jari na kasa da kasa dangane da yanayin kasuwanci na kasar. (Fa’iza)