Kotun amsar koke-koken zabe, ta amshi Koke-Koke guda takwas da suke kalubalantar zabukan kujerun ‘yan majalisun tarayya da na jihohi da hukumar zabe INEC ta gudanar a ranakun 25/2/2023 da 18/3/2023, a jihar Adamawa.
Rahotanni sunyi nuni da cewa ‘yan takarar jam’iyyar APC shida, suka garzaya kotun suna neman da kotun da rusa zabukan ‘yan majalisun tarayyar, da’aka bayyana da cewa na PDP ne.
Haka kuma cikin bukatun da ‘yan takarar jam’iyyar APC suka shigar gaban kotun sun bukaci da kotun da rusa zaben kujerar dan majalisar dattawa, mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, da kakakin majalisar dokokin jihar Aminu Iya Abbas, yayi nasarar lashewa.
Kujerun ‘yan majalisun wakilan tarayyar da ‘yan takarar APC suka shigar gaban kotun sun hada da dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Mubi ta kudu,Mubi ta arewa da Maiha da Jingi Rufai ya lashe da kuma kananan hukumomin Gombi,Hong da James Barka, ya lashe.
Sauran koke-koken da ke gaban kotun su ne; Abba Girei, (Muhammad Salihu) mai wakiltar Yola ya arewa, Yola ta kudu da Girei, da Muhammad Inuwa Bassi mai wakiltar kananan hukumomin Mayo-Belwa,Jada,Ganye da Toungo, da Zakaria Dauda Nyampa kananan hukumomin Michika da Madagali.
Da yake mika koken gaban kotun Sanata Abdul’aziz Nyako, ya roki kotun da ta rusa zaben kakakin majalisar dokokin jihar Aminu Iya Abbas da sauran mutum biyar da su ka yi nasara karkashin jam’iyyar PDP a zaben.
A bangare guda kuwa Rev. Amos Kumai Yohanna na jam’iyyar PDP ya na kalubalantar nasarar Sanata Ishaku Abbo, sanata mai wakiltar Adamawa ta arewa a karkashin jam’iyyar APC.
A takardar koken da Rev Amos ya gabatar gaban kotu mai lamba EPT/AD/SEN/02/2023, yayi zargin zaben Ishaka Cliff Abbo ya saba doka bisa dogaro da sabbin dokokin zaben 2022.