Akalla dakarun sojin Nijeriya hudu ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku a kauyen Lago da ke karamar hukumar Darazo a Jihar Bauchi.
Wasu mutane 13 sun samu raunuka daban-daban a hatsarin da ya rutsa da wata mota kirar Toyota.
- Gwamnati Ce Ta Yi Min Magudin Zabe Da Karfin Soji – Matawalle
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 24.2 Don Samar Da Intanet Kyauta
Hatsarin na zuwa ne sa’o’i bakwai bayan mutuwar mutane biyar a wani hatsarin mota da ya faru a kauyen Panshanu da ke kan babbar hanyar Toro zuwa Bauchi.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya alakanta musabbabin hatsarin da fashewar tayar motar bas din ta yi.
“Mutane 17 da hatsarin ya rutsa da su, dukkansu maza ne kuma dakarun sojin Nijeriya da ke kan hanyarsu ta zuwa Abuja.
“Hudu daga cikinsu sun rasa rayukansu nan take yayin da wasu 13 suka samu raunuka wasu kuma suka samu karaya,” in ji shi.
Abdullahi ya kara da cewa, an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na babban asibitin Darazo, yayin da wadanda suka jikkata kuma aka kai su Asibitin Kwararru da ke Bauchi domin yi musu magani.
Kwamandan sashen ya shawarci masu ababen hawa da su kasance masu lura da ka’idojin ababen hawa a ko da yaushe yayin da suke tuki.