Kasa da sa’o’i 48 bayan wata gobara ta kone kaya na miliyoyin Naira a kasuwar da ke Legas, wata gobara ta sake ta shi a kasuwar Olowu da ake sayar da kayan motoci da ke yankin Ikeja cikin Jihar Legas.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa gobarar wadda ta tashi a ranar Alhamis da misalin karfe 2:30 na rana ta lalata kaya na miliyoyin Naira ta kuma kone shaguna 12 da ake adana kaya da wani gidan sayar da abinci.
- Bayan Ficewar Ayu, PDP Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Fayose, Shema Da Anyim
- Zababben Gwamnan Kano Ya Nada Sakataren Yada Labaransa
Da yake magana kan lamarin, jami’in hukumar NEMA da ke Jihar Legas, Ibrahim Farinloye, ya ce ba a san abind a ya haddasa gobarar ba har sai an kammala bincike.
A cewarsa, shugaban kasuwar, Bassey Ikpendu ya bayyana cewa wani da ke kwana a kasuwar ne ya ga tashin gobarar amma kafin a ankare ta kama ko ina, inda aka yi gaggawar kai rahoto ga hukumar kashe gobara kuma suka zo a kan lokaci suka kashe ta, inda ya ce, babu wanda ya rasa ransa ko wani da ya samu rauni.
Ibrahim, ya ce shugaban ya kuma yaba da kokarin da hukumar kashe gobarar ta yi wajen zuwa a kan lokaci don lashe gobarar.
A cewarsa, NEMA ta ziyarci wajen don gano abin da ya haddasa gobarar.