Wani mai hannu da shuni da ke zaune a Jihar Kaduna, wanda bai bukaci a ambaci sunan sa ba, ya rabar da zakkar kudi ga masu kananan sana’o’i sama da 50 don su kara bunkasa harkokin kasuwancinsu.
Akasarin wadanda suka amafana da zakkar mata ne da kuma matasa da ke yin sana’o’in aski, sayar da abinci, yin tukwane, masu wankin kai, takalma da yin sana’a a kafar internet da sauransu.
Daya daga cikin daraktocin cibiyar samar da daidaito a tsakanin mabiya addinin musulunci da na kirista, Mallam Abdullahi Mohammed Sufi ne ya rabar da zakkar kudin a madadin wannan bawan Allah.
A hirasa da manena labarai jin kadan bayan rabar da zakkar, Sufi ya ce wanda ya bayar da zakkar kudin bai son a ambaci sunnan sa. Ya ce mutumin ya yanke shawarar bayar da zakkar kudin ne ga wadanda suka amfana don su kara bunkasa harkokin kasuwancinsau kuma su ci gaba da zama masu dogaro da kansu, musamman idan aka yi la’akari da yadda masu kanannan sana’o’i a jihar ke fuskantar kalubale masu yawan gaske.
Sufi ya yi kira ga sauran musulmi masu hannu da shuni da ke a daukacin fadin kasar nan da su taimaka wa masu kananan sana’o’i don su kara habaka kasuwancinsu ta yadda suma a nan gaba za su iya taimaka wa sauaran. Sannan ya yi kira musamman ga gwamnatin tarayya da ta samar da kyakyawan yanayi ga masu kananan sana’o’i da ke a kasar nan don su samu damar yin kasuwanci yadda ya kamata.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da zakkar, Nafisa Zakari Ya’u wacce ke yin kasuwanci ta kafar internet a Kaduna ta gode wa wanda ya ba su kudin, inda ta ce zakkar za ta taimaka mata wajen kara habaka kasuwancinta da kuma magance kalubalen da take fuskanta a baya
Ta yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su talllafa wa masu kanannan sana’o’i da jari don su ci gaba da zama masu dogaro da kansu, musamman duba ga yadda ake fuskantar kalubale a fannin kasuwanci a kasar nan.