Assalamu Alaikum Dr, Ina da tambaya game da hadisin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akan wani mutum da ya sadu da matar sa da rana cikin Ramadan, duba da yadda Manzon Allah ya warware masa matsalarsa, to idan har an sami wani ya sadu da matarsa da azumin kuma ba zai iya azumi ba, ‘yanta wuyaye, ciyarwa, kuma bai sami wanda zai ba shi abin da zai ciyar ba yaya zai yi? Allah ya saka da alkairi.
To dan’uwa kissar da ka fada ta zo a Hadisi tabbatacce mai lamba ta : 616 a cikin Sahihil Bukhari, sai dai malamai sun yi sabani akan mas’alar zuwa zantuttuka guda biyu:
1. Kaffarar ba za ta fadi akansa ba, za ta wanzu har zuwa lokacin da zai samu damar yin daya daga cikinsu, kamar yadda suke a jere a hadisin, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin hadisin bai ce masa kaffara ta fadi akansa ba, ya yi masa shiru ne.
2. Kaffarar ta fadi a kansa, saboda lokacin da ya ce ba zai iya ba, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bar masa dabinon don ya ciyar da iyalansa. Wasu malaman suna rinjayar da zance na karshe, saboda shi ne ya fi dacewa da zahirin hadisin. Don neman karin bayani duba : Al–minhaaj na Nawawy 3\182-183 Allah ne mafi sani.