Ranar 30 ga watan Maris, ma’aikatar harkokin wajen kasar Honduras ta sanar da cewa, shugabar kasar Xiomara Castro, za ta ziyarci kasar Sin nan ba da dadewa ba. Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki 4 kacal, bayan Honduras ta katse huldar diflomasiyya da Taiwan, tare da kulla hulda da kasar Sin.
Kafin kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Honduras, hukumomin Taiwan karkashin jam’iyyar DPP, sun yi kokarin daidaita lamura a tsakaninsu da Honduras, inda har suka nemi kasar Amurka ta shiga tsakani. Sai dai, duk irin kokarin da Taiwan da Amurka suka yi, bai cimma nasara ba.
Hukumomin Taiwan karkashin jam’iyyar DPP sun dade suna kiyaye huldarsu ta diflomasiyya ta hanyar amfani da dalar Amurka. Ko a baya-bayan nan, an bankado batutuwan amfani da dala a harkokin diflomasiyyar Honduras da Taiwan, ciki har da wanda ya shafi sama da dalar Amurka miliyan 20.
A watan Nuwamban shekarar 2021, bayan shugaba Castro ta Honduras ta bayyana cewa, za ta nemi kulla hulda da Sin yayin yakin neman zabenta, nan da nan mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Brian Nichols ya garzaya Honduras, inda ya furta a fili cewa, yana fatan Honduras za ta ci gaba da hulda da Taiwan. A watan Janairun bana ne kuma, Amurka ta shigar da jam’iyyar DPP cikin wani shiri da ya kunshi bangarorin 3, domin taimakawa Honduras.
Sai dai, sakamako ya sake tabbatar da cewa, ‘yancin Taiwan ba abu ne mai yuwuwa ba, kuma ba za a yi aminta da bangarorin waje ba. Shekaru 7 bayan Tsai Ing-wen ta kama aiki a matsayin jagorar hukumomin Taiwan, adadin wadanda ke huldar diflomasiyya da yankin ya ragu daga 22 zuwa 13. Wato karin kasashen duniya na kara amincewa da manufar Sin daya tak a duniya da kuma goyon bayan dinkewar kasar baki daya. Wannan shi ne yanayin da ake ciki a yanzu. (Fa’iza Mustapha)