Tsohon Sakataren Kunjiyar ‘Yan Jaridu ta kasa (NUJ) Midat Joseph, ya bayyanna cewa, zaben gwamna da aka yi na jihar Kaduna a kwanan baya cike yake da rudani.
Midat, wanda kuma shi ne mawallafin Jaridar ‘Kakaki Reporters’ ya yi ce sakamakon zaben ya saba da wanda yake a manhajar tattara sakon zabe ta hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.
- Masu Sa Ido Sun Bukaci INEC Ta Sake Nazarin Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kaduna
- INEC Na Fuskantar Matsin Lamba Don Sake Duba Zaben Kano, Kaduna Da Ogun
Midat ya ce, INEC a cikin mako daya ta sauke hakikanin sakamakon zaben gwamna na jihar Kaduna daga cikin manhajar IReV, inda hakan zai iya sanya was a shigar da kara gaban Kotu.
Dan Jaridar ya yi kira da a hukunta wadanda suka kitsa hakan kan sakamakon zaben gwamnan jihar, inda ya kara da cewa, akwai bukatar INEC ta yi nazari kan sakamakon domin ma’aikatanta ne suka taimaka wa ‘yan siyasa wajen yin magudin zabe.
Midat, ya buga misali da mazabar Makera da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta kudu, inda sojoji suka karbe sakamakon zaben aka kuma hana ‘yan jarida shiga cikin cibiyar.
Midat ya ce, idan har ba’a kawo karshen wannan rashin adalcin ba, to ba makawa zai je kotu don ganin an hukunta irin wadannan mutanen da ya danganta su da shedanu.