Ina mai farin cikin sanar da ku cewa na yi murabus daga matsayina na shugaban jam’iyyar NNPP na kasa daga yau Juma’a 31 ga Maris, 2023.
Bisa la’akari da abubuwan da suka faru a baya, da lokacin da kuma bayan babban zabukan da aka gudanar a ranakun 25 ga Fabrairu da 18 ga Maris, 2023, lallai na fahimci cewa, jam’iyyarmu ta NNPP tana da kyakkyawar makoma da kuma damar da za ta iya fitowa a matsayin babbar jam’iyyar siyasa da za ta iya yin nasara na lashe zaben shugaban kasa da duk sauran zabuka a 2027.
Don cimma wannan, dole ne mu fara shirye-shirye don tunkarar kalubalen da ke gaba. Kuma lokaci ya yi da jam’iyyar mu, za ta bukaci manyan sauye-sauye a dukkan matakai na jam’iyyar domin karfafa tushenta, da inganta karfin gudanar da ayyukanta da kuma kara habakata ta yadda za ta kere wa sauran jam’iyyun siyasa 17 da ke karkashin INEC.
Na tabbata, dole ne wannan canjin ya fara daga gare ni. Wannan shi ne dalilin da ya sa na yanke shawarar ajiye mukamina don ba sabbin jini dama.
Da wannan wasika, ina kuma sanar da jagoranmu na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ‘yan kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da daukacin mambobinmu na kasa baki daya cewa ni har yanzu ina nan kuma zan ci gaba da kasancewa mai gaskiya a cikin jam’iyyarmu.