Sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a da babban bankin kasar Sin ya fitar ya nuna cewa, adadin Sinawa masu burin kashe karin kudade sabanin zuba jari, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2023 ya karu idan an kwatanta da na rubu’in karshe na bara.
Binciken wanda aka gudanar kan masu ajiyar kudade a bankuna 20,000 dake biranen kasar 50, ya nuna karuwar kaso 23.2 bisa dari na Sinawa masu fatan kashe karin kudade a watanni ukun farko na bana, adadin da ya haura na watanni ukun karshen shekarar bara da kaso 0.5 bisa dari.
A daya hannun kuma, adadin masu burin zuba jari a wa’adin ya kai kaso 18.8 bisa dari, adadin da ya karu da kaso 3.3 bisa dari idan an kwatanta da na rubu’in da ya gabaci hakan.
A bangaren masu fatan kara zuba jari, binciken ya nuna sun fi mayar da hankali ga hidimomin kudade da bankuna ke samarwa, da hidimomin da dillalai ke samarwa, da harkokin inshora, sai kuma fannin sanya kadarori cikin asusun amintattu da sayen hannayen jari.
Su kuwa Sinawa masu fatan kashe karin kudade, sun fi ba da karfi a fannonin hidimomin samar da ilimi, da kiwon lafiya, da yawon shakatawa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)