Gwamnatin tarayya ta caccaki wasu kasashen yammacin duniya kan yadda suke cigaba da alaka da kungiyar ta’addanci ta IPOB.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, wanda ya yi wannan zargin a birnin Washington DC a lokacin da yake ganawa da wasu kungiyoyin yada labarai na kasa da kasa da cibiyoyin siyasa, ya ce munafuncin kasashen yammacin duniya ne da su ke ikirarin yaki da ta’addanci amma sai suka koma suna goyon bayan ‘yan ta’adda kamar kungiya IPOB.
Ministan ya je Washington ne don tattaunawa da kungiyoyin watsa labarai na kasa da kasa kan zaben 2023 da aka kammala
Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai na kasashen waje da su daina amfani da farfaganda a shafukan sada zumunta kan zaben Nijeriya na 2023 a matsayin hujjar buga wani labari kan zaben.
Ya ce, dole kafafen yada labarai na kasashen yamma su rika bincikan rahoton da suka samu a shafukan sada zumunta kafin su buga labarin a shafukansu. (NAN)