Wata kungiyar matan musulmi mai suna ‘yan uwa a Aljannah (Sisters of Jannah) ta bayyana damuwarta kan yawaitar rabuwar aure a tsakanin ma’aurata musulmi a Arewacin Nijeriya.
Kungiyar ta bayyana damuwarta ne a taronta na Ramadan karo na biyu da aka shirya a Bauchi mai taken “Batun Sakin aure a gidajen Musulmi/Hakkin makwabtaka.” Daily trust ta rahoto.
Babbar bakuwar, Malama Khadija Ahmed ta koka kan yadda galibin iyaye sukan yi watsi da umarnin Alkur’ani mai tsarki wajen aurar da ‘ya’yansu.
Malamar ta shawarci ma’aurata da su guji son kai, son zuciya, nuna isa sannan kuma su koyi halin juriya da yafiya da warware sabani cikin adalci da tsoron Allah.
Anata bangaren, Shugabar kungiyar, Hajiya Maryam Garba Bagel ta shawarci ma’aurata da kada su kasance masu son kai da son zuciya, su yi kokari su kasance masu adalci a juna domin gina gidan aure nagari.