Yayin da Nijeriya ke kara kusantar ranar 29 ga watan Mayu, da za a rantsar da zababben shugaba kasa, kungiyar Ohanaeze Ndigbo, ta fitar da wasu bukatu hudu da ta ke so Bola Tinubu, ya cika domin kwantar da hankalin ‘yan kabilar Igbo.
Babban Sakataren kungiyar Ohanaeze, Okechukwu Isiguzoro, ya ce ya kamata Tinubu ya saki Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafra (IPOB), ba tare da wani sharadi ba.
- Sin: Fannin Sayayya Da Na Yawon Shakatawa Na Kara Farfadowa A Rubu’in Farko Na Bana
- Gwamnatin Kaduna Ta Sassauta Dokar Zirga-Zirga Da Ta Saka A Wasu Yankuna
Isiguzoro, ya ce sakin Kanu zai dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, dole ne Tinubu ya tabbatar da yankin Kudu maso Gabas ya samar da shugaban majalisar dattawa.
Jigon na Ohanaeze, ya ce dole ne Tinubu ya tabbatar da ganin an kirkiri jiha ta shida a yankin kudu maso Gabas.
A cewar Isiguzoro: “Tinubu mai son ci gaba ne, shi mai dabara ne; gwamnatin Tinubu ba za ta zama kamar gwamnatin Buhari ba.
“Matsalar Tinubu, ita ce yawan shekaru, da kuma mafi yawan mutanen da suka sa Buhari bai yi nasara ba suna bayansa saboda wasu kalubalen da ya ke fuskanta biyo bayan zaben 2023.
“Dole ne Tinubu ya tabbatar wa da yankin Kudu maso Gabas wadannan muhimman bukatu hudu don yankin ya amince da shi a matsayin shugaban Nijeriya, kana kabilar Igbo su tsaya tsayin-daka su kare mulkinsa.
“Na farko shi ne, dole ne Tinubu ya maido da zaman lafiya da tsaro ba tare da wani sharadi ba ta hanyar sakin Nnamdi Kanu, ko zai ba shi afuwar shugaban kasa a lokacin jawabin karbar mulkinsa ko kuma ya yi amfani da karfin ikon shugaban kasa wajen ganin an sake shi domin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin kudu maso gabas.
“Na biyu, dole ne Tinubu ya fara aikin warkarwa wurin ganin ya daidaita tikitin Musulmi da Musulmi a takarar shugaban kasa ta hanyar bai wa Kirista daga Kudu maso Gabas shugaban majalisar dattawa. Duk wanda zai zama Shugaban Majalisar Dattawa ka da ya zama wani Sanata mai mukami a majalisar wadanda ba shi da kishin kasa.
“Muna kira ga majalisar dattawa da ta gyara dokokinta tare da ba da izinin sababbin ‘yan majalisa su jagorancin majalisar saboda Sanatocin da ke rike da mukamin akwai shakku a kan su kuma ba za su iya kare muradun Ndigbos (kabilar Igbo) ba.
“Na uku, dole ne Tinubu ya sanya tsarin siyasa da zai tabbatar da cewa ‘yan kabilar Igbo sun ga alkawarin da Buhari ya yi masu a asirce cewa zai tabbatar da yankin ya samu jiha ta shida.
“Dole ne zababben shugaban kasa ya tabbatar da cewa dukkan kofofin tattalin arziki a fadin kasar nan da suka hada da sake bude mashigar ruwa ta Kalaba, yaye kogin Azumiri, yi wa ‘yan kungiyar IPOB afuwa, da kuma biyan diyya ga iyalan da aka kashe tsawon shekaru.”