Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, a matsayinsu na masu fafutukar tabbatar da cudanyar sassa da karfafa tsarin demokuradiyya a hadin gwiwar kasa da kasa, kasashen Sin da Faransa suna da kwarewa da nauyin da ya rataya a wuyansu na kawar da bambance-bambance da abubuwan dake iya kawo tarnaki, da kiyaye alkiblar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare mai dorewa, da cin moriyar juna, da samun nasara tare, kuma mai kuzari.
Xi ya bayyana hakan ne, Alhamis din nan a lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.
Shugaba Xi ya ce, a yau duniya tana fuskantar gagarumin sauyi da ba a taba gani ba a tarihi, yana mai cewa, kasashen biyu wato Sin da Faransa, a matsayinsu na mambobin din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kana manyan kasashen dake da al’adar ‘yancin kai, ya kamata su aiwatar da tsarin hadin gwiwa na hakika, domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma wadata a duk duniya.
A yau din ne kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Faransa Emmanuel, suka gana da manema labarai bayan tattaunawar da suka yi.
Xi Jinping ya ce, Sin na nacewa ga matsayin ingiza warware rikicin Ukraine ta hanyar shawarwari da kuma a siyasance. Sin na fatan hadin kai da Faransa don yin kira tare ga kasashen duniya da a ci gaba da kai zuciya nesa, da kuma tsayawa tsayin daka kan martaba dokar jin kai ta kasa da kasa da cika alkawarin da aka yi na hana amfani da makaman nukiliya, da farfado da shawarwari nan da nan.
Xi kuma ya ce, kamata ya yi bangarori daban-daban su hada kansu don kaucewa illar da rikicin zai haifarwa fannin hatsi da makamashi da hada-hadar kudi da zirga-zirga da sauransu, takaita illar da rikicin zai kawowa kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa. (Mai fassarawa: Ibrahim)