Daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Maris, an shirya wani taron tattaunawa da ya shafi tsarin demokuradiyya a birnin Beijing na kasar Sin, wanda ke da taken “Demokuradiyya: Fa’ida ta bai daya ga daukacin bil-Adama. Wannan biki da aka gudanar da shi a karo na biyu, ya hallara daruruwan baki daga kasashe da yankuna fiye da 100, da kuma kungiyoyin kasa da kasa.
Mahalarta taron sun amince cewa, demokuradiyya wani abu ne mai muhimmanci ga daukacin bil-Adama, kuma akwai abubuwa da dama dake tabbatar da demokuradiyya. Don haka, ya kamata kasashe su mutunta bambance-bambancen wayewar kai na duniya, da mutunta hanyoyin sauran kasashe na bunkasa demokuradiyya, da karfafa mu’amala da ilmantarwa, da kara gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.
Amsoshin masana da ’yan siyasa na kasashen Afrika ga tambayar “ Mene ne tsarin demokuradiyya?”
Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, yana cikin bakin da aka gayyata don halartar taron. Ya kuma gaya wa wakilin CMG cewa, kalmar “demokuradiyya” ba ta da ma’ana, idan an kasa lura da tarihin wata kasa, da yanayin da wata al’umma ke ciki. A cewarsa, tushen demokuradiyya shi ne, a ba jama’a damar halartar aikin mulki, da ba su ikon yanke shawara, da na sa ido kan ayyukan dake gudana, gami da haifar musu da alfanu.
Mista Onunaiju ya kara da cewa, babu wani salo na bai daya game da tsarin demokuradiyya, saboda haka, ya kamata a lura da wasu darajoji da jama’ar wata kasa suke dora wa muhimmanci, da raya tsarin demokuradiyya, bisa tarihi da al’adu na musamman na wannan kasa.
A nasa bangare, shugaban jam’iyyar gurguzu, wato Socialist Party a Turance, ta kasar Zambiya, Dokta Fred M’membe, ya ce, tsarin demokuradiyya ya shafi ’yancin wata al’umma na tabbatar da makomar kanta, da ikon mulkin kai, da mutunci na wata kasa da na al’ummarta. A cewarsa, ba za a taba samun tsarin demokuradiyya na gaske ba, a wata kasar da ta kasance karkashin sarrafawa da shawo kai na sauran kasashe, ta yadda ba ta da cikakken iko na mulkin kai. Saboda jama’ar wannan kasa ba za su samu ’yancin bayyana ra’ayi ba, kuma ba za su iya tabbatar da makomar kai ba.
Ban da wannan kuma, Kugiza Kaheru, mamban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Uganda, shi ma ya yi tsokaci kan ma’anar tsarin demokuradiyya, inda ya ce, kamata ya yi, tsarin demokuradiyya ya samar da taimako ga jama’a, a kokarinsu na neman samun biyan bukata. Ya ce, tsarin demokuradiyya na gaske shi ne wanda ya sa al’ummar wata kasa samun damar cimma babban burinsu.
Ra’ayoyin masana da ’yan siyasa na kasashen Afrika kan tsarin demokuradiyya na kasar Sin
Ban da wannan kuma, wadannan masana da ’yan siyasa na kasashen Afrika sun bayyana ra’ayoyinsu, dangane da tsarin demokuradiyya na kasar Sin. Inda mista Charles Onunaiju ya ce, cikakken tsarin dimokuradiyya da yake damawa da dukkan jama’a a kasar Sin, wata babbar nasara ce da jama’ar kasar Sin baki daya suka cimma karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Demokuradiyya ce da ke mai da hankali kan jin dadin jama’a, da nufin ci gaba da inganta yanayin rayuwarsu.
Charles Onunaiju ya ce, a Afrika, ana mai da hankali sosai kan tsarin demokuradiyya da mulkin demokuradiyya wanda ke jaddada dokoki, amma ba a mayar da hankali sosai wajen taimaka wa mutane tunkarar kalubalen rayuwa. A cewarsa, yana fatan dukkan kasashe, musamman kasashe masu tasowa na Afirka, za su nazarci cikakken tsarin demokuradiyyar jama’ar kasar Sin, wanda ya kunshi jama’a a dukkan matakai, kuma su fahimci cewa, demokuradiyya ba wai kawai ta kunshi ka’idojin aiki ba ne, har ma da bukatar biyan hakikanin bukatun jama’a.
Mista Onunaiju ya kara da cewa, kasar Sin tana raya tattalin arzikinta cikin matukar sauri, inda ayyukan raya kasa da ta gudanar da su cikin shekaru 45, suka yi daidai da ayyukan da su kasashen yamma suka yi cikin shekaru fiye da 250. Ba za iya yin aiki da sauri kamar haka ba, in ba tare da samun cikakken goyon baya daga jama’a ba, inda suke nuna kuzari, da kokarin halarta ayyuka daban daban, da taka muhimmiyar rawa wajen samar da nagartattun manufofin da kasar ke bukata. Hakan ya shaida cewa, alkawarin da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta yi, na mai da moriyar jama’a a gaban komai, ya cika. In ji Mista Onunaiju.
A nasa bangare, Dokta Fred M’membe daga kasar Zambia, ya bayyana cewa, a kasar Sin, ana iya ganin cikakkiyar darajar tsarin demokuradiyya, wato nuna damuwa da jin dadin bil-adama, da kuma nuna damuwa ga mafi yawan jama’a, ba wai kawai masu sukuni ba.
A cewarsa, akwai attajirai da yawa a kasar Sin, amma ba masu arziki ne suke tsara manufofin gwamnatin kasar ba, maimakon haka, ana tabbatar da matakan gwamnatocin kasar ne bisa muhimman muradun al’ummar Sinawa.
Mista M’membe ya kara da cewa, kasar Sin ta samu nasarar fid da dukkan al’ummarta daga kangin talauci cikin wani wa’adin lokaci mafi gajarta a tarihin duniya, kana ba ta taba yin mulkin mallaka a sauran kasashe, ko kuma kwatar duyiyoyinsu ba. Wannan babbar nasarar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin dan Adam ta nuna cewa, tabbas ne akwai cikakken tsarin demokuradiyya a kasar. Wannan demokuradiyya ita ce wadda kasar Sin ta yi kokarin raya ta, bisa tushen tsarin siyasa na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin.
Sa’an nan a nasa bangare, Kugiza Kaheru, dan siyasar kasar Uganda, ya ce, tsarin demokuradiyyar kasar Sin, ya samo asali ne daga tushen tarihi da al’adu, kuma jigonsa shi ne ci gaba da koyo, da ci gaba da koyi daga sauran sassa, da ci gaba da daidaitawa, da raya kasa, da kuma samun bunkasuwa bisa sauyin zamani.
Demokuradiyyar kasar Sin ba ta da tsauri da ra’ayin mazan jiya, amma tana da kyau wajen daidaita bukatun al’umma. Ba kawai a ka’idance take ba, ita ma ta shafi ayyuka na zahiri, in ji Mista Kaheru.
Daukaka demokuradiyya a harkokin kasa da kasa
Ta yaya ake iya daukaka tunanin demokuradiyya a harkokin kasa da kasa? Wannan tambaya tana janyo hankalin masana, da ’yan siyasar kasashen Afrika, da suka halarci taron tattauna batun demokuradiyya da ya gudana a birnin Beijing na wannan karo. Inda Mista Charles Onunaiju ya ce, daga lokacin baya, har zuwa yanzu, ana ta ganin yadda wasu manyan kasashe suke neman yin babakere a duniya, inda suke wa sauran kasashe danniya don a bi umarninsu. Sai dai wannan yunkuri ya kan ci tura. Ya ce, a kasashe daban daban da suka hada da Iran, da Libya, da Afghanistan, da dai sauransu, an shaida yadda ba za a samu nasara ba, ta hanyar cusa wani nau’in tsarin demokuradiya ga sauran kasashe.
A nasa bangare, mista Fred M’membe daga kasar Zambia, ya ambaci hanyar da ya kamata a bi, don tabbatar da darajar demokuradiyya a harkokin kasa da kasa. A cewarsa, kamata a yi, a koyi manufofin da kasar Sin ta dauka wajen kula da al’amuran kasa da kasa, wadanda suka hada da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, da kokarin kulla huldar da za ta amfani dukkan bangarorin masu ruwa da tsaki, da girmama wayewar kai da al’adu daban daban da aka samu a duniyarmu, da amincewa da niyyar duk wata al’umma ta neman zamanintarwa ta wata hanyar da ta dace da al’adu da tarihin ta.
Masana da ’yan siyasa na kasashen Afrika, su ma sun bayyana ra’ayoyinsu kan Shawarar Wayewar Kai ta Duniya, wadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, ganin yadda shawarar ta shafi yadda za a kula da huldar kasa da kasa, da al’amuran kasa da kasa, ta wata hanyar da ta dace da ra’ayin demokuradiyya. Inda mista Fred M’membe daga kasar Zambia ya ce, Shawarar Wayewar Kai ta Duniya wani nagartaccen tunani ne, wanda zai taimakawa dan Adam a kokarinsa na tabbatar da ci gaban duniya.
A cewar mista M’membe, cikin wannan shawarar da aka gabatar, an jaddada bukatar girmama dukkan kasashe, da sauraron ra’ayoyin dukkan bangarori, ba tare da lura da bambancin karfinsu ba. Ya ce, wannan ra’ayi, shi ne hanya daya tilo da za a iya bi don tabbatar da zaman lafiya a duniya. Idan kuma an yi watsi da wannan hanya, tabbas za a samu rikici tsakanin kasashe da al’ummu daban daban.
Sa’an nan, a nasa bangare, Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya, ya ce, Shawarar Wayewar Kai ta Duniya da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, za ta haifar da alfanu ga daukacin bil Adama. A cewarsa, Shawarar Wayewar Kai ta Duniya ta jaddada muhimmancin samun cudanya tsakanin al’ummu da al’adu daban daban, don tabbatar da fahimtar juna, da girmama juna, da kulawa da juna a tsakaninsu, ta yadda za a samu karin hadin kan al’ummun duniya, tare da samar da tsaro da walwala ta bai daya, wadanda za su amfani daukacin bil-Adama.
Sakamakon da aka samu bisa tattaunawar da aka yi a wajen taron
Kamar yadda dan siyasar kasar Uganda Kugiza Kaheru ya fada, a wajen taron da ya shafi tunanin demokuradiyya da ya gudana a kasar Sin, tsarin demokuradiyya ya yi kama da abun sha da ake kira da “ice cream”, wato ya kamata ya kunshi dandano da nau’o’i daban daban, don biyan mabambantan bukatu na mutanen duniya. Kuma masana da ’yan siyasa mahalarta taron sun cimma ra’ayi daya, wato ya kamata a yarda da kasancewar nau’o’in tsarin demokuradiyya daban daban a duniya, kana ya kamata tsarin demokuradiyya ya taimakawa biyan bukatun jama’a. Ban da haka kuma, sun ce kasar Sin ta riga ta kama tafarkin demokuradiyya mai fadi, kuma ta ba da gudummawar hikimar kasar Sin ga ci gaban siyasar bil-Adama.
(marubucin bayanin: Bello Wang, wakilian sashen Hausa na CMG)