• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Manhajar Gmail A Wayoyin Android (kimiyya)

by Ibrahim Sabo
2 years ago
in Kimiyya Da Fasahar Sadarwa
0
Amfanin Manhajar Gmail A Wayoyin Android (kimiyya)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Manhajar Gmail daya ne daga cikin ’email serbice probider’ da kamfanin Google ke gudanar da shi. Ga mai amfani da wayar Android ‘email’ na kamfanin Google (Gmail) zai fi yi masa amfani fiye da sauran ‘probiders’ irinsu Yahoo, Hotmail, Yanded, outlook da sauransu.

Da yawan mutane in an ce Google, sukan takaita shi da ‘searching engine’ ma’ana wurin da za ka yi browsing (bincike) na wani abu, in kuma aka ambaci ‘Gmail’, da yawa mukan takaita aikinsa da turawa ko karbar sakon ‘email’ da ajiye lambar waya, amma duk amfaninsa ya wuce nan.

  • Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

Google shi ne kamfanin da yafi kowane kamfani karfi a duniyar fasahar sadarwa. Shi ne kamfani da yake gudanar da OS (operating system) na Android tare da shi da sauran wasu kamfanoni. Android shi ne OS da mafi yawancinmu muka fi amfani da shi a wayoyinmu na Samsung, Pidel, Tecno, Infinid, Itel, Diomi, Gionee, Huawei, HTC, Motorola, Oppo, Nokia, Bibo da sauransu.

Idan ka bude ‘Gmail Account’ kai tsaye ka yi rijista ne ‘Google account and services, ma’ana za ka yi amfani da duk wani tsare-tsare da manhajoji 131 da Google ke gudanar da su (about.google/products), wadanda iya mai Google account ne kadai zai iya morarsu kai tsaye dari bisa dari.

Wadannan manhajojin sun hada da Gmail, Playstore, YouTube, Google Dribe, Photos, Blogger, Forms, Alerts, AdSense, Google Chats, Google classroom, Family Link, Find My Debice, Google Groups, Contacts, Message, Google one, Podcast, Hangouts, Scholar, Meet, AdMob, Cloud, Translate… da sauransu. Kuma ana amfani da su wajen tura sakonni, karatu, kasuwanci, debeloping, taruka, adana bayanai, kididdiga da sauransu.

Labarai Masu Nasaba

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

Mallakar ‘Google account’ yana taimaka wa wajen Auto-Fill na Login Credentials (bayanai da za ka shiga domin bude wani shafi, wato (username da password); ma’ana, idan ka yi sabing bayanan shiga wani shafi (kamar Facebook ko Twitter), babu bukatar sai ka yi typing na ‘username da password’, a’a kai tsaye Auto-Fill zai shigar maka da bayanan.
Ba za mu iya bayanin dukkan ‘Manhajoji 131′ ba a yanzu, ba kuma lalle a ce sai ka iya amfani da dukkanin manhajojin ba (ya danganta da wanda kake bukatar amfani da shi), sannan wasun su ba a iya amfani da su a wasu kasashen.

Ga bayanin wasu atakaice:
PLAYSTORE– Rumbu ne mai dauke da manhajojin Android (apk) 2.59 million (Statista, 2022). Mai Google account (Gmail) ne kadai zai iya shiga domin sauke ‘apps’ daga cikin Play store.

GOOGLE CONTACTS – ‘App’ ne da ake iya adana lambobin waya daga 1 zuwa 25,000. Amfani da ‘Google Contact’ na da matukar muhimmanci, saboda ko an sami akasi wayarka ta bata, ko lalace, ko aka sace, da zarar ka sami wata wayar ko a computer za ka iya dawo da duk ‘lambobin wayarka’ da ka adana (sabing) a cikinsa.

BLOGGER– zaka iya kirkirar ‘blog site’ da Blogger, har kana iya wallafa rubutu kyauta.

Idan kana samun traffic da yawa, za ka iya ‘rijista’ da ‘AdSense’ ka fara samun kudin da Blogger din, musamman idan kana dora talla/ads (misali, leadership.blogspot.com).
FIND MY DEVICE – manhaja ce da za ta taimaka wajen gano inda wayarka take, idan ka rasa ta, ko ka jefar, ko aka sace.
YOUTUBE – wannan sananne ‘app’ ne na Google da za ka iya bude ‘channel’ da shi ta hanyar amfani da ‘Google Account’. Idan kana samun traffic da yawa, akalla subscribers 1000. kuma aka samu an bude ‘contents’ na ka kamar sau 4000, za ka iya fara samun kudi da YouTube.
GOOGLE PHOTOS – Wannan manhajar tana taimaka wa sosai wajen adana hotunan cikin waya. Idan kana ‘backup’ na hotuna a cikin ‘Photos’ za a iya ‘restoring’ nasu a kowace irin waya ka canza, a kowane lokaci.
GOOGLE DRIVE – wannan manhajar ‘cloud’ ce da ke iya bawa mutum damar ajiye ‘files’ a ciki. Suna bawa kowane user (mutum) ‘storage’ na 15 gigabytes. Za ka iya bude abubuwa da ka adana a cikin Dribe a kowace waya ko computer idan ka yi amfani da ‘Google Account’ (Gmail) naka.

SCHOLAR – Google scholar kamar ‘Google searching engine’ ne. Yana taimaka wa wajen lalubo metadata (ta rubuce-rubuce na ilimi).
Misali, idan ka sami wani rubutu, kuma kana son ba shi ‘reference’ idan ka dauki ‘jumla’ ka dora a scholar zai baka irin wannan jumlar ta bayyana a rubuce-rubuce da suka gabata, cikin littattafai, ko mukala (articles), ko journals, ko mujalla da sauransu.
CHROME REMOTE DESKTOP – manhaja ce da za ta ba ka damar shiga cikin files na computer daga wayarka, ko da ba ka tare da computer din.

GOOGLE ADS – Manhajar AdSense da AdMob na taimaka wa masu amfani a social media yin rijista domin samun kudi ta hanyar dora talla a shafukansu (ads).
MEETS – Kamar zoom yake, ana iya yin meeting online.
Akwai sauran apps na Google da za su taimaka sosai wajen debeloping, kamar optimize, Google Analytics, Google Cloud, Firebase, Flutter, Play Protect, Play Games, Surbey, Web da sauransu.

Akwai apps na Google da za su taimaka wajen editing na hoto, SNAP SEED da PHOTOS. Akwai na duba taswira (map), GOOGLE MAP da GOOGLE EARTH. Akwai manhajar karbar bayanai ta GOOGLE FORMS, akwai manhajar fassara ta TRANSLATE. Akwai manhajoji da yawa na GOOGLE, sai a hankali ko in bukata ta tashi, za mu dauki wasu muna bayaninsu a takaice.

Yawancin wadancan tsare-tsare na Google, iya masu Google account (Gmail) ke iya morarsu sosai. Ana iya amfani da Gmail, kamar sauran ‘probiders’ (Yahoo, Hotmail…) wajen yin rijista ko cike-ciken da ake yi a yanar gizo, kamar bude profile na makaranta ko cike aiki (job application), ko cike tallafi, misalin, surbibal fund da sauran cike-cike. Kar ka yi gangancin ba wa kowa Login details na Gmail naka, domin za a iya shiga (accessing) dukkan wadancan tsare-tsaren da shi.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Xi Jinping Ya Kai Rangadi A Lardin Guangdong

Next Post

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Anambra, Mbadinuju Ya Rasu

Related

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

4 weeks ago
Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

2 months ago
Hanyoyin Kare Kanka Daga Damfara Ta Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Hanyoyin Kare Kanka Daga Damfara Ta Intanet

3 months ago
Yadda Za A Kare Yara Daga Barazanar Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Yadda Za A Kare Yara Daga Barazanar Intanet

3 months ago
Mantuwa Na Matukar Taimakon Rayuwar Mutane – Masani
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Mantuwa Na Matukar Taimakon Rayuwar Mutane – Masani

7 months ago
Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk

7 months ago
Next Post
Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Anambra, Mbadinuju Ya Rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Anambra, Mbadinuju Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

May 15, 2025
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

May 15, 2025
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

May 15, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

May 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

May 15, 2025
An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

May 15, 2025
HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

May 15, 2025
Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

May 15, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.