A yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba wata sabuwar roka ta kasuwanci samfurin Hyperbola-1.
Rokar wadda wani kamfani mai zaman kansa dake birnin Beijing mai suna Interstellar Glory ya kera, an harba ta ne da misalin karfe 12 na rana daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin.
Manufar harba rokar gwajin, ita ce tabbatar da tsarin rokar da kuma tattara bayanai kan yadda take aiki. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp