Sabbin alkaluma daga hukumar kudaden musayar ketare ta kasar Sin na nuna cewa, a karshen watan Maris da ya gabata, yawan kudaden musayar ketare da kasar ke da su, ya kai dala biliyan 3183.9, wanda ya karu da dala biliyan 50.7 ko kashi 1.62 cikin 100 kwatanta da karshen watan Fabrairu.
Jami’in hukumar ya nuna cewa, Sin tana nacewa ga samun bunkasuwa mai dorewa da daidaiton tattalin arziki mai inganci kuma tana da kyakkyawan fatan samun bunkasuwa, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton ma’aunin ajiyar kudaden wajenta. (Amina Xu)
Talla
Talla