Wakili na musamman kan harkokin Asiya da BRICS na kasar Afirka ta Kudu, Anil Sooklal, ya bayyana wa babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a jiya cewa, an riga an tabbatar da cewa, shugabannin dukkan kasashe membobin kungiyar BRICS, za su halarci taron kolin kungiyar da zai gudana a karshen watan Agustan bana a Afirka ta Kudu.
A cewar Sooklal, shugaban Rasha, Vladimir Putin ya riga ya samu goron-gayyata daga takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, kana ba shi da wata niyyar kin amincewa. Afirka ta Kudu na himmatuwa wajen shirya gudanar da wani kasaitaccen taron kolin BRICS. (Murtala Zhang)