Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yaba wa dakarun sojin Operation Forest Sanity bisa nasarar da suka samu na hallaka kasurgumin dan bindiga, Isiya Danwasa a karamar hukumar Igabi a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 1, Sun Harbe Wasu 2 A Kano
- An Haramta Wa Limamai Karanta Alkur’ani Daga Waya A lokutan Sallolin Dare A Kuwait
Danwasa ne musabbabin kashe-kashen jama’a da yin garkuwa da mutane da kuma sace shanu a wasu yankunan jihar.
Sun samu nasarar kashe shi ne a yayin wani kwanton-bauna da dakarun suka kai yankin Sabon Birni da ke a karamar hukumar Igabi.
El-Rufai ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da ka da su gajiya wajen bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai don ci gaba da magance kalubalen rashin tsaro a jihar.