Wani Dansanda mai suna Nura Mande, mai aiki a bangaren sufuri, ya mayar da makudan dalolin da ya tsinta a lokacin da ake Tantance maniyyatan hajjin bana a sansanin Hukumar Alhazai ta jihar Katsina.
Mande ya tsinci Dala 800, guzurin wata maniyyaciya daga Ƙaramar hukumar Kusada mai suna Hadiza Usman Chamiya, inji rahoton kafar yada Labarai ta Katsina city News.
Mande ya damka Wannan kudi ga hukumar Alhazai ta hannun Daraktan sashen mulki na hukumar, Alh Sada Salisu Rumah, inda aka damka wa maniyyaciyar kudinta.
Bayan mayarwa maniyyaciyar da kudinta, Alh Sada Rumah ya yaba da kyawon hali da Gaskiya da Mande ya nuna.
Ya ce shugaban hukumar Alhaji Suleimnan kuki zai sanar da rundunar yansandan jihar katsina kan Wannan hali na kwarai da ya nuna.