Ana ci gaba da samun tashin hankali biyo bayan yawaitar hare-haren ta’addanci tun bayan kammala babban zaben 2023 da tabarbarewar kudaden da hakan ya janyo durkushewar tattalin arzikin kasar.
A yayin da aka samu kwanciyar hankali a ci gaba da gudanar da zabukan dangane da munanan hare-haren ta’addanci. Amma a yanzu dai ba haka lamarin yake ba domin an sake samun sabbin hare-hare kan al’ummomin da ba su ji dadi ba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan ‘yan Nijeriya da suka hada da mata da kananan yara, wanda al’ummar Binuwai ne suka fi fuskantar matsalar.
- Xi Jinping: Turbar Zamantarwa Ta Kasar Sin Tana Da Manufa, Tsare-tsare Da Dabaru
- IMF: Tattalin Arzikin Sin Zai Karu Da Kaso 5.2 A 2023
Kananan Hukumomin Apa, Agatu, Otukpo da Guma ne suka fi yawan asarar rayuka a harin na Jihar ta Benue.
Rahotanni sun nuna cewa Karamar Hukumar Apa kadai ta samu asarar rayuka sama da 250, yayin da mutum kasa da 75 suka rasa rayukansu a Karamar Hukumar Otukpo a wannan lokaci.
Karamar Hukumar Agatu, wacce a da ita ce cibiyar hare-haren makiyaya a Benuwe ta Kudu, an samu karancin hare-hare tare da raunata kusan mutum 30.
Sauran wuraren da abin ya shafa sun hada da Ikpobi, Odugbo, Ugbobi Akpanta, Ologba, Oyiji da Imana a Karamar Hukumar Apa. Oshigbudu Atakpa da Okpagabi da ke Agatu su ma lamarin ya rutsa da su.
Maharani kuma sun kai hari cocin Pentecostal na Kirista da ke Akenawe, Tswareb a gundumar Ukemberagya/Tswareb dake Karamar Hukumar Logo, inda suka kashe wani mai ibada tare da yin garkuwa da limamin cocin da wasu masu ibada.
Wannan harin ya biyo bayan kisan da aka yi wa basaraken al’ummar Ugbobi a Karamar Hukumar Apa, wanda aka kashe shi tare da wasu mutane da dama.
Haka kuma an kai hari kauyen Umogidi da ke gundumar Enetekpa Adoka a Karamar Hukumar Otukpo inda ‘yan bindigar suka kashe mutum uku da farko. Jim kadan bayan binne su, maharan sun sake komawa kauyen, inda suka kashe mutum 51.
A daidai lokacin da jama’a suka nuna damuwarsu kan kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar Umogidi, maharan sun kai farmaki makarantar firamare ta LGEA, Mgban, da ke unguwar Nyieb Council a Karamar Hukumar Guma, inda basaraken al’ummar yankin, ya rasa ‘ya’ya biyu a harin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin. An samu mutuwar mutum 37 yayin da wasu 37 da suka hada da yara da mata suka samu munanan raunuka.
Shugaban al’ummar Ucha, Zaki John Akpan, ya zargi sojojin gwamnatin da aka tura jihar da hada baki da su; ya kuma zargi sojoji da zuba ido kan kashe mutanen da ake yi masa.
Don haka ya yi kira da a janye sojoji tare da tura jami’an ‘yan sandan tafi da gidanka da jami’an Cibil Defence a yankin domin kare ‘yan kasa.
“Idan gwamnati na son taimaka wa wannan al’umma, ya kamata gwamnati ta janye sojoji zuwa bariki, sannan ta tura ‘yan sandan sintiri da jami’an tsaron farin kaya,” in ji shi. Sannan ya yi watsi da rade-radin cewa dokar hana kiwo ce da ta aka kafa tun 2017 ce ta haddasa hare-haren.
“Abin da ya faru a nan, mutane suna danganta hakan ga dokar hana kiwo amma mu da muke nan ba ma ganin dokar a matsayin dokar hana kiwo. In kuma mutane sun fadi haka, sai mu tambaye su me ke faruwa a jihohin Kaduna, Taraba da sauran jihohin su ma hana kiwo ne ya sa ake kai musu hare-hare?
Me suke cewa, amma kuma a can ana kashe-kashe? Sun ce sun baza jami’an tsaro a wadannan wuraren, ba wai ina kalubalantar su ba amma wadannan matsalolin suna ci gaba da wanzuwa. Ina mamakin me ya sa rashin tsaro ke cigaba da wanzuwa duk da kasancewar jami’an tsaro.
“Za mu sanar da ku cewa a nan ne wadannan mutane (‘yan ta’adda) suke. Makiyaya dauke da makamai sun ce muna cinye musu shanunsu amma a nan Ngban da suka zo kashe mutum 37, babu shanu guda da wani ya taba musu. Kwanaki uku kafin harin, sun zo kiwo a kusa da gidajenmu da bindigogi, sojoji za su gan su da bindigogi amma ba za su ce da su komai ba.
A ranar zabe, makiyaya sun kashe mutum 12 a Tse Alaar, washegari suka far wa Yelewata, daga baya suka kashe wani a Udei wanda ya je rafi don yin wanka. Bayan haka sai suka zo Tse Ikyogen suka bude gidajen mutane suka fitar da dawa don shanunsu su ci, haka abin ya faru a Tse-Iho. Idan muka kai rahoto ga sojoji za su ce kada mu dame makiyayan, amma za su duba.”
Ya ce yayin da tazarar da ke tsakanin Ngban da Keana ya kai kusan kilomita 50, babu kowa a cikin daji amma filin bai wadatar da makiyayan da ke dauke da makamai ba, ya kara da cewa kawai suna son kashe kowa ne a Benuwe.
“Ina jin cewa makiyayan suna da wata manufa ta daban. Magana a kan dokar hana kiwo, babu wanda ya nemi makiyaya su bar Binuwai; gwamnati kawai ta nemi su yi kiwo. Suna da dokoki a wasu jihohin da suka haramta barasa da wasu kuma mutane suna biyayya.
Me ya sa ba za su iya bin dokar Benue ba? Wannan harin na jiya mun zakulo gawarwaki 36 yayin da mutum 38 suka jikkata. Daya daga cikin wadanda suka jikkata shi har ma ya fid da rai, inda adadin wadanda suka jikkata ya kai 37. Sun kona wata mota da babura biyu a harabar hakimin, sannan sun kona wani gida mai ciyayi tare da ciyawar dawa, yayin da suka janye sai suka rika kashe mutane,” in ji shi.
‘Yan Gudun Hijirar Da Suka Tsira A Sansanin Hamada Na Benue
A halin da ake ciki, ‘yan gudun hijirar da suka tsira da rayukansu a makarantar Firamaren LGED, Ngbam, a gundumar Nyieb ta Karamar Hukumar Guma a Jihar Benue, sun tsere daga sansanin saboda fargabar sake kai hari.
Shugaban Karamar Hukumar Mike Uba, wanda ya bayyana haka ga Wakilinmu, ya ce duk da cewa an samu kwanciyar hankali saboda kasancewar hadin gwiwar jami’an tsaro da aka tura yankin, amma duk da haka duk ‘yan gudun hijirar sun fice daga sansanin saboda fargabar sake kai musu hari.
“An tura tawagar jami’an tsaron hadin gwiwa a sansanin domin dawo da zaman lafiya amma kamar yadda nake magana da ku a yanzu, babu ko daya daga cikin ‘yan gudun hijira a sansanin. Na je can da safe, na ga sansanin babu kowa, da na yi tambaya, sai aka ce mini wasu sun je su zauna tare da ‘yan uwansu, wasu kuma da ba su da inda za su je sun tafi sansanin ‘yan gudun hijira na Ortese.”
Da aka tambaye shi game da gawarwaki 38 da aka ajiye a dakin ajiyar gawa na Daudu, shugaban ya ce an binne duk wadanda aka kashe a harin kamar yadda gwamna, Dakta Samuel Ortom ya ba da umarni.
Haka kuma, babban daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Benue (BSUTH),
Makurdi, Farfesa Terrumun Swende, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa duk wadanda suka samu raunuka daban-daban a harin suna karbar magani, inda ya kara da cewa an samu rahoton mutuwa.
Jadawalin Hare-Hare, Kashe-Kashe Bayan Babban Zaben 2023
Sabbin hare-hare da kashe-kashen da kungiyoyin ‘yan ta’adda daban-daban suka yi a Nijeriya na kara ta’azzara tun bayan babban zaben kasar nan da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu.
Ga Wasu Hare-Hare Na Kashe-Kashen Da Aka Yi Cikin Kwanaki 42 Da Suka Gabata
A ranar 4 ga watan Maris: ‘Yan bindiga sun kai hari shalkwatar Karamar Hukumar Zamfara, sun kashe DPO da wasu mutum 2.
‘Yan bindigar wadanda a yawansu suka afka wa Maru, sun yi ta harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin ficewa daga yankin domin tsira da rayukansu.
Da samun labarin harin, jami’in ‘yan sanda reshen Karamar Hukumar Kazeem Raheem, ya tattara mutanensa da wasu ‘yan banga na yankin domin fatattakar ‘yan bindigar, sai dai an kashe DPO da wani Sajan mai suna Rabiu Bagobiri da wani dan banga mai suna Shehu.
A ranar 8 ga Maris:
Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutum 50 ne ‘yan ta’adda suka sace.
Wata mata mai juna biyu tare da wasu mutum biyar aka ruwaito cewa ‘yan ta’adda sun kashe su a unguwannin Karamar Hukumar Rafi da Wushishi a Jihar Neja.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyukan jin kai na jihar, Mista Emmanuel Umar, ya ce har yanzu gwamnati ba ta tantance cikakken bayanin harin ba.
Sannan a ranar 8 ga watan Maris:
Rundunar ‘yansanda Jihar Barno ta tabbatar da kisan wasu masunta 29 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar.
Harin da ka kaddamar a kauyen Mukdolo dake yankin Gamborun Ngala na jihar, wasu daga cikin masuntan da abin ya rutsa da su suna asibiti cikin mawuyacin hali.
Kakanin Rundunar ‘Yansandan jihar, Sani Kamilu, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ya ce lamarin ya faru ne a ranar takwas ga watan Maris din 2023 ne.
Kazalika a ranar 12 ga watan Maris:
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun afka wasu garuruwa shida a Kwande, Jihar Binuwai, inda suka kashe akalla mutum 50.
A’ummomin da abin ya shafa a harin da aka kai kwanaki hudu sun hada da Adam, Iyarinwa, Abamde Ityulub, Waya Boagundu, Agura Ayaga da kuma yankin mazabar Azege Turan na Karamar Jumar Kwande.
Tosohon Shugaban Karamar Hukumar Tertsua Yarkbewan, wanda ya tabbatar da faruwar haka, ya ce adadin wadan da suka mutu a wannan lamarin yana iya karuwa.
A ranar 15 zuwa 17 ga Maris:
An kai wani sabon hari a al’ummar Neja, inda ya rutsa da sojoji hudu da wasu mutum shida da bindiga suka hallaka.
Kazalika ‘yan bidiga sun sake kaddamar da wani sabon hari kan wasu al’ ummomimi a Jihar Neja, inda suka kashe mutum 11 gami da wani sojan Nijeriya mai mukamin manjo da wasu sojojin uku.
Bugu da kari harin ya rutsa da mambobin kungiyoyin sa-kai shida da ‘yan bindigar suka kashe.
‘Yan bindigar sun kashe mutane cikin kwanaki biyu tare da yin garkuwa da mutanen kauyen da bai gaza mutum 60 ba a lokacin da suka kai farmakin.
A ranar 24 ga Maris 24:
Makiyaya dauke da makamai suka kai hari kan wata al’ umma a Ondo, inda suka sace mutane suka yi wasu kisan gilla.
Wasu makiyaya dauke da bindigu sun kai hari kan al’ummar Ogbese a jihar Ondo, inda aka yi garkuwa da wasu mazauna yankin yayin da wasu suka samu munanan raunuka.
Lamarin wanda ya faru a ranar Juma’a, 24 ga watan Maris, ya jefa daukacin garin cikin fargaba da fargaba yayin da iyalan wadanda aka sace ke jiran jin ta bakin masu garkuwar.
Shedun gani da ido sun ce makiyayan sun yi amfani da adduna wajen kutsawa wasu mazauna yankin a yayin harin da aka kai.
Wasu makiyaya dauke da bindigu sun kai hari kan al’ummar Ogbese a Jihar Ondo, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna yankin yayin da wasu suka samu munanan raunuka.
Harin ya faru a ranar Juma’a, 24 ga watan Maris, inda ya jefa daukacin jama’ar garin cikin fargaba yayin da iyalan wadanda aka sace ke jiran jin ta bakin masu garkuwar.
Shaidun gani da ido sun ce makiyayan sun yi amfani da adduna wajen kutsawa wasu mazauna yankin a yayin harin da aka kai.
A ranar 2 ga Afrilu: Mutum hudu sun rasa rayukansu sakamakon wata arangama tsakanin ‘yan kungiyar IPOB da ‘yansanda a garin Aba.
A ci gaba tada kayar baya da ‘yan kungiyar IPOB ke yi. Mutum hudu sun rasa rayukansu sakamakon wata arangama tsakanin ‘yan kungiyar IPOB da ‘yansanda a garin Aba.
Sannan aka sake wata sabuwar arangama tsakanin ‘yansandan Nijeriya da mambobin kungiyar OPOB inda aka kashe wa ‘yan kungiyar mutum hudu.
‘Yansandan sun bayyana cewa, ‘yan kungiyar ne suka kai musu hari clash between the Nigeria Rundunar ‘yan sandan ta yi ikirarin cewa ‘yan kungiyar ta IPOB sun kai wa mutanen su hari a wani sintiri na tabbatar da tsaro a cikin babban birnin Aba.
Ranar 4 ga Afrilu:
‘Yan ta’addar Boko Haram sun kashe Pasto, tare da jikkata wasu jama’a cikin wani kauye a Borno
A yammacin ranar Talata ne ‘yan ta’addar Boko Haram dauke da makamai suka kai farmaki kauyen Mathdaw da ke Karamar Hukumar Biu a Jihar Borno inda suka harbe wani Fasto da aka sakaya sunansa wanda ke kula da Cocin ‘Yan’uwa da ake kira EYN.
‘Yan ta’addar, a cewar majiya mai tushe, sun kuma harbi matar faston wacce a halin yanzu take kwance a asibiti da ba a bayyana inda yake ba.
A ranar 5 ga watan Afrilu:
Makiyaya sun kai hari kan wata bas inda suka kashe fasinja, suka kuma suka yi awon gaba da wasu mutum 8 a Delta
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari kan wata motar bas Toyota Sienna, inda suka kashe fasinja daya tare da yin garkuwa da wasu mutum takwas a tsakanin al’ummar Ndemili da Oliogo, a Karamar Hukumar Ndokwa ta Yamma a Jihar Delta.
An gano cewa motar tana jigilar fasinjojin ne daga Onitsha, Jihar Anambra a ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu, yayin da ‘yan bindiga suka yi mata kwanton bauna da misalin karfe 5 na yamma.
Wata majiya ta ce an harbe fasinja daya inda ya mutu nan take, yayin da aka yi garkuwa da wasu aka kutsa da su cikin daji.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Mista Bright Edafe, ya ce ‘yan bindiga ne da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai harin.
A Ranar 5 Afrilu: An Kashe Mutane 46 A Otukpo, Jihar Benue
Wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kai wani mummunan hari kan al’ummar Umogidi da ke gundumar Entekpa Adoka na Karamar Hukumar Otukpo ta Jihar Benue. Sabon harin ya zo ne kwana guda bayan da wasu da ake zargin makiyaya ne suka mamaye al’umma tare da kashe mutane uku a wasu raneku.
Mai ba Gwamna Samuel Ortom shawara kan harkokin tsaro, Laftanar Kanal Paul Hemba (mai ritaya), ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici da radadi.”