Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta kira wani taron manema labarai a jiya Alhamis, don bayyana yadda ake rarraba albarkatun jiyya a duk fadin kasar. Ya zuwa yanzu, kasar ta kafa cibiyoyin kiwon lafiya na kasa guda 13 a wasu fannoni na musamman a fadin kasar, a sa’i daya kuma ta kafa cibiyoyin jiyya na shiyya-shiyya 76 a wasu warare dake da karancin kayayyakin kiwon lafiya.
Mataimakin darektan sashen kula da manufofin kiwon lafiya na hukumar kiwon lafiya ta kasar Li Dachuan ya ce, wadannan cibiyoyi sun samu gogewa matuka a fannin nazari. Daga baya, za a yi cikaken nazari don tsai da ajandar raya wadannan cibiyoyi da rarraba albarkatun jiyya yadda ya kamata, ta yadda za a warware gibin dake tsakanin wurare daban-daban a wannan fanni.
Jami’in ya bayyana cewa, asibitocin dake gundumomi sun samu ingantuwa sosai bayan samun taimakon da manyan asibitoci suka samar musu. Ya zuwa karshen shekarar 2022, kashi 87.7% na asibitoin gundumomi sun kai matsayin mataki na 2 a kasar Sin, ciki har da kashi 45.6% sun kai matsayin mataki na 3 a kasar. (Amina Xu)